Abdul-Aziz Nyako

Dan siyasar Najeriya

Abdul-Aziz Murtala Nyako (an haife shi ranar goma sha tara 19 ga watan Disamba shekarar alif dubu ɗaya da ɗari tara da saba'in 1970) ɗan majalisar dattawa ne a tarayyar Najeriya daga jihar Adamawa . Yana wakiltar Adamawa ta tsakiya a majalisar tarayya ta takwas 8 a yanzu.[1] Sanata Nyako shi ne shugaban kwamitin ayyuka na musamman na majalisar wakilai ta ƙasa ta takwas 8.[2]

Abdul-Aziz Nyako
mutum
Bayanai
Jinsi namiji
Shekarun haihuwa 18 Oktoba 1971
Wurin haihuwa Jihar Adamawa
Sana'a ɗan siyasa
Muƙamin da ya riƙe mamba a majalisar dattijai ta Najeriya
Ilimi a Jami'ar Tsaron Nijeriya
Ɗan bangaren siyasa African Democratic Congress (en) Fassara
Addini Musulunci

An zabi Nyako a matsayin sanata a majalisar wakilai ta takwas 8 a karkashin jam’iyyar APC amma daga baya ya sauya sheka zuwa jam’iyyar African Democratic Congress domin tsayawa takarar gwamnan Adamawa.[3] Ɗan tsohon gwamnan jihar Adamawa, Murtala Nyako.

Sanatan Adamawa ta tsakiya ya kunshi kananan hukumomi bakwai 7.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2020-05-07. Retrieved 2023-03-23.
  2. https://nass.gov.ng/mp/profile/525 Archived 2023-03-23 at the Wayback Machine
  3. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2019-03-09. Retrieved 2023-03-23.