Abdou Sidikou
Abdou Sidikou (An haude shi a shekarar 1927, ya rasu a shekarar 1973) ɗan siyasan Nijar ne kuma jami'in diflomasiyya. Sidikou shi ne Ministan Harkokin Wajen Nijar daga shekarar 1967-1970 a ƙarƙashin Hamani Diori.[1]
Abdou Sidikou | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Kouré, 1927 | ||
ƙasa | Nijar | ||
Mutuwa | 26 ga Yuli, 1973 | ||
Karatu | |||
Harsuna | Faransanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da Mai wanzar da zaman lafiya |
Rayuwar farko
gyara sasheAn haifi Abdou - sunan mahaifinsa a Kouré, Niger a 1927. A ƙarƙashin mulkin mallaka na Faransa ya kasance dan wani shugaban yankin da aka nada, ko Chef du Canton, ya yi karatu a fitaccen École normale supérieure William Ponty a Dakar sannan daga baya ya yi karatun Likita a Kwalejin Magunguna ta Paris, ya kammala karatunsa a shekarata 1956, kuma ya fara aiki a Asibiti na Seine [2] a Faris, sannan kuma ya zama babban Masanin harhaɗa magunguna a Asibitin Ƙasa (Niamey)
Ayyukan Gwamnati
gyara sasheA 1959, an nada Abdou a matsayin darektan majalisar minista na farko na Kiwon Lafiya na Diallo Boubakar, sannan a 1962 aka nada shi Jakadan Nijar a Amurka, Kanada, da Majalisar Ɗinkin Duniya. A 1964 ya koma Jamus, inda ya kasance Jakadan Nijar a Yammacin Jamus, Austria, da Benelux da Scandinavia, da ƙungiyar Tattalin Arzikin Turai . Ya zama Sakataren Ministan Harkokin Waje a Yamai, kuma a ranar 14 ga Afrilun shekarar 1967, ya karɓi aikin daga hannun Shugaba Hamani Diori . Saboda rashin lafiya, ya sa aka nada shi a matsayin "Sakataren Harkokin Waje na Shugaban Ƙasa" a watan Janairun 1970, a wancan lokacin yana matsayin mukamin minista. Ya mutu 26 Yuli 1973.
Manazarta
gyara sashe- ↑ He was a member of the ruling PPN-RDA party.Decalo, Samuel (1997). Historical Dictionary of the Niger (3rd ed.). Boston & Folkestone: Scarecrow Press. ISBN 0-8108-3136-8.:pp. 16–17
- ↑ "Hôpital privé de la Seine-Saint-Denis"