Zubeiru ko Zubayru dan Adama (ya rasu a shekarar 1903) shi ne sarkin masarautar Adamawa wanda mahaifinsa, Modibo Adama ya kafa. A lokacin da ya hau kan karagar mulki a shekarar 1890, masarutar ta samu barazana daga Jamusawa, turawan Faransa da Burtaniya. Zubeiru ya yi yunƙurin "matakin nuna rashin amincewa, duk da kwai kishi, amma kuma babu alamar nasar" kan zaluncin turawa na masarautu.[1]

Zubeiru bi Adama
Rayuwa
Haihuwa 19 century
Mutuwa ga Faburairu, 1903
Sana'a
Sana'a ruler (en) Fassara, ɗan kasuwa da slave trader (en) Fassara
Wurin aiki Kamerun (en) Fassara

Mulkinsa ya samu rauni a dalilin yaki da Hayatu bn Sa'id sannan kuma yayi yunkurin bijirewa kamfanin turawa wato Royal Niger Company da gwamnatin Birtaniya a karkashin Frederick Lugard. A shekarar 1901 an tilasta masa ya tsere daga Yola kuma ya zama dan gudun hijira.[2]

Manazarta

gyara sashe
  1. Victor T. Le Vine (1964). The Cameroons, from Mandate to Independence. University of California Press. p. 41.
  2. Mark R. Lipschutz; R. Kent Rasmussen (1989). "ZUBEIRU (d.1903)". Dictionary of African Historical Biography. University of California Press. pp. 255–6. ISBN 978-0-520-06611-3.