Zé Kalanga
Paulo Baptista Nsimba (an haife shi ne a ranar 12 ga watan Oktoban shekara ta 1983), ana yi masa lakabi da Zé Kalanga, tsohon ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Angola wanda ya taka leda a matsayin winger.[1]
Zé Kalanga | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Cikakken suna | Paulo Batista Nsimba | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Luanda, 12 Oktoba 1983 (41 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Angola | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Karatu | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Harsuna | Portuguese language | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Mahalarcin
| |||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | wing half (en) | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Nauyi | 67 kg | ||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||||
Tsayi | 170 cm |
Sana'a
gyara sasheWanda kuma aka sani da Ricardo Eloy ya fara aikinsa a kulob din Petro Atletico na Angola a garinsa na Luanda. [2] Ya buga wasansa na farko a tawagar kasar Angola acikin shekara ta 2003 da Gabon. [2] Kwallon da ya yi a Angola a gefen hannun dama a gasar cin kofin duniya ta 2006 ya sa ya koma kulob din Romanian Dinamo București inda a kakarsa ta farko ya kasance cikin tawagar da ta lashe gasar Liga I. [2] [3]
A gasar cin kofin duniya, Zé Kalanga ya zama gwarzon dan wasa a wasan da Angola ta buga da Iran a rukuninsu a ranar 21 ga watan Yuni, a wasan da abokin wasansa Flávio ya farke kwallon farko da suka tashi 1-1. [4]
A cikin watan Yunin shekara ta 2006 bai halarci wasan share fage na Dinamo ba bayan hutun bazara. Bayan haka an ba shi da aro ga kungiyar kwallon kafa ta Boavista ta Portugal na tsawon lokacin kakar 2007-08. [4]
An saka sunan shi a cikin 'yan wasan Angola da za su buga gasar cin kofin Afrika a Ghana a cikin shekara ta 2008 inda ya zo a madadinsa a wasan farko da Angola ta buga da Afirka ta Kudu. [2] Bajintar da ya yi ya sa aka tuno da shi a ka 'yan wasan goma sha dayan farko a wasa na biyu da Senegal inda ya buga cikakken minti 90 cikin salo mai kyau, inda ya zura kwallo a ragar dan wasan gaba Manucho a wasan da suka yi nasara da ci 3-1. [2]
Girmamawa
gyara sasheDinamo București
- Laliga 1 : 2006-07
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Ze Kalanga, "spartanul" dinamovist din Angola: fără "avion privat" și numere la mașină, mereu cu zâmbetul pe buze" [Ze Kalanga, the Dinamo "Spartan" from Angola: no "private plane" and numbers on the car, always with a smile on his face] (in Romanian). Theplaymaker.ro. 8 July 2020. Retrieved 23 March 2021.
- ↑ 2.0 2.1 2.2 2.3 2.4 Zé Kalanga at National-Football-Teams.com
- ↑ Samfuri:RomanianSoccerZé Kalanga at National-Football- Teams.com
- ↑ 4.0 4.1 Zé Kalanga at RomanianSoccer.ro (in Romanian)Empty citation (help)
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Girabola.com – Zé Kalanga Archived 2009-01-20 at the Wayback Machine
- Zé Kalanga ya koma Dinamo
- Zé Kalanga in CNN Archived 2012-11-03 at the Wayback Machine
- Zé Kalanga at Soccerway