Omoba Yinka Mursiq Durosinmi (an haife shi 25 ga watan Yunin shekara ta alif dari tara da sittin da daya 1961A.c) ɗan siyasar Najeriya ne kuma tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ojo ta jihar Legas.[1]

Yinka Durosinmi
Rayuwa
Haihuwa 25 ga Yuni, 1961 (63 shekaru)
ƙasa Najeriya
Harshen uwa Yarbanci
Karatu
Makaranta Jami'ar, Jihar Lagos
Lagos State University of Science and Technology
Harsuna Turanci
Yarbanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Rayuwar farko da ilimi

gyara sashe

An haifi Yinka Durosinmi a cikin gidan sarautar masarautar Osolu a Irewe, wani gari a Ojo, jihar Legas. Ya halarci makarantar sakandire ta Apapa Baptist, Apapa sannan ya yi karatun sakandire a Kwalejin Awori da ke Ojo, ya kuma ci gaba da samun Diploma ta ƙasa a fannin harkokin kasuwanci a Kwalejin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Legas, Isolo a yanzu Jihar Legas. Polytechnic. Ya kuma yi karatun digiri na biyu a fannin shari'a, shari'ar mulki da manufofin jama'a daga Jami'ar Jihar Legas, Ojo.[2]

Yinka ya kasance tsohon shugaban ƙaramar hukumar Ojo har zuwa shekarar 2014 lokacin da ya yanke shawarar tsayawa takarar wakilcin Mazaɓar Ojo a majalisar dokokin Najeriya ƙarƙashin jam’iyyar All Progressives Congress. Ya ci gaba da faɗuwa zaɓe bayan Tajudeen Obasa ya yi nasara.[3]

Rayuwa ta sirri

gyara sashe

Yinka shine ɗa ga Alhaji Remilekun Durosinmi, shugaban jam'iyyar All Progressives Congress a yankin Ojo/ Badagry na jihar Legas. Ƴar uwarsa Gimbiya Sarah Sosan tsohuwar mataimakiyar gwamnan jihar Legas ce. Yana da aure da ƴaƴa.[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. https://thenationonlineng.net/ex-chairman-secure-apc-ticket-ojo-federal-constituency/
  2. "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2016-03-04. Retrieved 2023-03-16.
  3. 3.0 3.1 https://www.newtelegraphng.com/in-the-shadow-of-parents/[permanent dead link]