Yawon Buɗe Ido a Cikin Comoros

Comoros ba ta da masana'antar yawon buɗe ido mai ƙarfi.

Yawon Buɗe Ido a Cikin Comoros
tourism in a region (en) Fassara
Bayanai
Facet of (en) Fassara Yawon bude ido

Lambobin yawon buɗe ido

gyara sashe

Kodayake Comoros na da albarkatun kasa da yawa don yawon buɗe ido, irin su rairayin bakin teku da yanayin ruwa, ba ta da ƙarfin masana'antar yawon buɗe ido kamar yadda masu fafatawa a yankin Réunion, Mauritius, da Seychelles. Karancin sana'arta na yawon bude ido ya samo asali ne saboda rashin tsaro na siyasa, tare da tashe-tashen hankula na siyasa a cikin shekaru talatin da suka gabata. [1]

Masu yawon bude ido a cikin Comoros galibinsu ’yan Amurka ne da kuma Turawa masu arziki, yayin da yawancin jarin otal-otal suka fito daga Afirka ta Kudu. [2]

Abubuwa masu jan hankali na yawon bude ido

gyara sashe

Manyan wuraren yawon bude ido a cikin Comoros sune rairayin bakin teku, kamun kifi, da yanayin tsaunuka.[3] Mohéli wuri ne mai ban sha'awa na yawon bude ido. Grand Comore yana da filin jirgin sama na ƙasa da ƙasa da mafi yawan 'yan otal ɗin Comoros. [2]

Manazarta

gyara sashe
  1. Travel and Tourism in Comoros, Euromonitor
  2. 2.0 2.1 Boniface, Brain G.; Christopher P. Cooper (2001). Worldwide Destinations: The Geography of Travel and Tourism . Butterworth-Heinemann. p. 252. ISBN 0-7506-4231-9 Empty citation (help)
  3. Africa South of the Sahara 2004. Taylor & Francis Group, Routledge. 2003. p. 256. ISBN 1-85743-183-9.

Hanyoyin haɗi na waje

gyara sashe