Yassir Al-Dosari

Limamin Masallacin Ka'aba

Yasir bin Rasyid ad-Dousary ( Larabci: ياسر بن راشد الدوسري‎  ; An haife shi a ranar 6 ga watan Agustan shekarar 1980, limami ne, khatib (wato mai khuduba), kuma Alaramma ya fito daga Saudi Arabia. Ya kasance daya daga cikin limaman Masjid al-Haram tun 12 ga watan Oktoba shekarar, 2019. A baya, ya kasance yana jagorantar sallah Tarawih da Tahajjud a Masjid al-Haram daga shekarar, 2015 sannan kuma yayi limanci a masallatai da dama a Riyadh tun a shekarar, 1995. Al-Dosari dalibi ne na kungiyar malamai da shehunai, wadanda suka hada da Abdulaziz Al Sheikh, Saleh Al-Fawzan, da Abdullah ibn Jibrin . Ya kuma koyi qira’a tare da shehunnai da qariwa da dama, daga cikinsu akwai Bakri Al-Tarabisyi da Ibrahim Al-Akhdar.[1][2][3]

Yassir Al-Dosari
Rayuwa
Haihuwa Al-Kharj (en) Fassara, 6 ga Augusta, 1980 (43 shekaru)
ƙasa Saudi Arebiya
Karatu
Makaranta King Saud University (en) Fassara
Sana'a
Sana'a qāriʾ (en) Fassara da Liman

Sana'a gyara sashe

Limamin Masjid Al-Haram gyara sashe

A ranar 29 ga watan Sha’aban shekara ta, 1436 A H (15 ga watan Yunin shekarar, 2015), Sarki Salman bin Abdulaziz ya ba da umarnin Al-Dosari ya zama daya daga cikin limamin Tarawih da Tahajjud a Masjid Al-Haram a lokacin Ramadan. Ya bi wannnan umarni na tsawon shekaru biyar. A ranar 13 Safar 1441 A H (12 watan Oktoba shekarar 2019), Sarki Salman ya nada Sheikh Yasir a matsayin limamin dindindin a Masjid Al-Haram. Ya jagoranci sallar farko a Masallacin Harami a lokacin Sallar Magariba da Isha'i a ranar Asabar 13 ga Oktoba shekarar, 2019.

Baya ga kasancewarsa limami, Al-Dosari yana cikin masu ba da shawara ga fadar Shugabancin Masallacin Haramain tun daga shekarar, 2020. An nada shi wannan mukamin ne bayan Abdul-Rahman Al-Sudais, Shugaban Janar na Shugabancin Haramain, ya yanke shawarar sake tsara mukaman hukumar ba da shawara ta wannan hukuma.

Mai Khudubah a Masallacin Harami gyara sashe

Bayan kimanin shekaru uku da zama limamin masallacin Al-Haram, Sheikh as-Sudais ya sanar da cewa an nada Al-Dosari a matsayin khatib na Masjid Al-Haram tare da amincewar Sarki Salman a watan Disamba shekara ta, 2022.

Manazarta gyara sashe

  1. "د. ياسر الدوسري". Manarat al-Haramain. Retrieved 7 December 2022.
  2. "تعيين ياسر الدوسري إماما للمسجد الحرام والحذيفي للنبوي". الفجر. 12 October 2019. Archived from the original on 19 May 2022. Retrieved 19 May 2022.
  3. Nuhait, Abdullah (12 October 2019). "الدوسري" يرفع الشكر للقيادة بعد تعيينه في إمامة الحرم المكي"". Sabq (in Larabci). Retrieved 7 December 2022.