Yash Pal Ghai CBE (an haife shi a ranar 20 ga watan Oktoba shekara ta 1938) masanin ilimin Kenya ne a fannin dokar tsarin mulki. Tun daga shekara ta 2007 shi ne shugaban sashin ba da shawara kan tsarin mulki na shirin ci gaban Majalisar Ɗinkin Duniya a Nepal. Har zuwa shekara ta 2008, ya kasance Wakili na Musamman na Babban Sakatare Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya a Cambodia kan kare hakkin ɗan Adam. A cikin watan Satumba na 2008, ya yi murabus daga muƙaminsa, sakamakon takaddama mai zafi da gwamnatin Cambodia. [1] Ya kasance Fellow of the British Academy tun a shekarar 2005.

Yash Ghai
United Nations Special Rapporteur (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa Nairobi, 20 Oktoba 1938 (85 shekaru)
ƙasa Kenya
Karatu
Makaranta Harvard Law School (en) Fassara
Jami'ar Oxford
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a Malami
Employers University of Warwick (en) Fassara
Yale Law School (en) Fassara
Uppsala University (en) Fassara
University of Dar es Salaam (en) Fassara
Kyaututtuka
Mamba British Academy (en) Fassara
Imani
Jam'iyar siyasa independent politician (en) Fassara

Rayuwar farko da ilimi gyara sashe

Kakanninsa sun fito ne daga rukunin dangin Khukhrain na Khatris, waɗanda suka fito daga yankin Punjab na Arewacin Indiya, kuma suna cikin tafiye-tafiyen hijirar Indiya a Gabashin Afirka, wanda Daular Burtaniya ta ɗauki nauyinsa. Mahaifinsa ya tura Ghai zuwa Jami'ar Oxford don yin karatu.[1]

Sana'a gyara sashe

Ya kasance Sir YK Pao Farfesa na Shari'ar Jama'a a Jami'ar Hong Kong wanda ya fara a shekara ta 1989. Ya kasance Farfesa mai girma a can tun lokacin da ya yi ritaya a shekarar 2005. Kafin wannan, Ghai ya koyar kuma ya yi bincike a fannin shari'a a Jami'ar Warwick, Jami'ar Uppsala a Sweden, Cibiyar Shari'a ta Duniya a Birnin New York, da Makarantar Yale Law. Ya kuma koyar da darussa a Jami'ar Wisconsin Law School, a matsayin wani ɓangare na shirin musayar.[2] Shi ne shugaban kwamitin sake duba kundin tsarin mulkin Kenya (wanda ya yi ƙoƙarin rubuta kundin tsarin mulkin Kenya na zamani) daga shekarun 2000 zuwa 2004. Kwanan nan ne gwamnatin Soja ta Fiji ta zaɓi Farfesa Ghai a matsayin Shugaban Kwamitin Tsarin Mulki na Fiji.

Ghai ya kuma ba da shawara da taimaka wa kungiyoyi masu zaman kansu kan ayyukan da suka shafi dokokin kare hakkin ɗan adam. Ya tsara Yarjejeniya ta Haƙƙin Bil Adama ta Asiya—Yarjejeniya ta Jama'a, aikin Hukumar Haƙƙin Dan Adam ta Asiya.

Ghai ya rubuta littattafai da yawa kan doka a Afirka, tsibiran Pacific, da sauran wurare. 

Girmamawa da kyaututtuka gyara sashe

Farfesa Ghai ya sami kyautuka da girmamawa kamar haka:

Girmamawa gyara sashe

Kyauta gyara sashe

  • 2001: Kyautar Distinguished Research Achievement Award from the University of Hong Kong

Girmamawa gyara sashe

  • Jami'ar Kudancin Pacific, Digiri na girmamawa, 1995
  • Society for Advanced Legal Studies, Honorary fellow, 1997
  • Law Society of Kenya, Honorary Life Member, 1998
  • Queen's University, Canada, Honorary Doctorate of Laws (LLD), 2014

Manazarta gyara sashe

  1. "Professor Yash Ghai C.V." (PDF). University of Hong Kong. Retrieved 31 March 2013.
  2. "Scholarly Exchange and Visitors - University of Wisconsin Law School".
  3. Yash Pal Ghai Not found in London Gazette 1969-1991