William Kwasi Sabi
William Kwasi Sabi (an haife shi 23 ga watan Agusta , shekarata 1966) ɗan siyasan Ghana ne kuma memba na Majalisar Bakwai na Jamhuriyyar Ghana ta huɗu mai wakiltar mazabar Dormaa Gabas a yankin Brong-Ahafo akan tikitin New Patriotic Party (NPP).[1]
William Kwasi Sabi | |||||
---|---|---|---|---|---|
7 ga Janairu, 2017 - District: Dormaa East Constituency (en) Election: 2016 Ghanaian general election (en)
7 ga Janairu, 2013 - 6 ga Janairu, 2017 District: Dormaa East Constituency (en) Election: 2012 Ghanaian general election (en) | |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | 23 ga Augusta, 1966 (58 shekaru) | ||||
ƙasa | Ghana | ||||
Karatu | |||||
Makaranta |
University of Ghana Digiri a kimiyya : business administration (en) Jami'ar Cape Town master's degree (en) : public health (en) | ||||
Harsuna | Turanci | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | ɗan siyasa da health economist (en) | ||||
Imani | |||||
Addini | Kiristanci | ||||
Jam'iyar siyasa | New Patriotic Party |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Sabi a ranar 23 ga Agusta, 1966. Ya fito ne daga Wamfie a yankin Bono na Ghana. Ya yi digirin farko na Kimiyya a fannin Gudanarwa a Jami'ar Ghana Legon da kuma digiri na biyu a fannin Kiwon Lafiyar Jama'a daga Jami'ar Cape Town.[1][2]
Aiki
gyara sasheSabi ya fara aikinsa a matsayin mai kula da asibiti a ma’aikatar lafiya ta Katolika, Sunyani daga 1997 zuwa 2003. Ya yi aiki a matsayin malami a Kwalejin Jami’ar Katolika ta Ghana daga 2005 zuwa 2009. A 2008, ya zama manajan ayyuka na Hukumar Inshorar Lafiya ta Kasa. Daga baya ya yi aiki a matsayin mai ba da shawara kan gudanarwa tare da MDF West Africa Limited.[3]
Siyasa
gyara sasheSabi ya tsaya takarar kujerar mazabar Dormaa ta Gabas a kan tikitin New Patriotic Party a zaben 2012 kuma ya yi nasara. Ya samu kuri'u 13,712 wanda ke wakiltar kashi 56.87% na yawan kuri'un da aka kada, don haka ya doke sauran 'yan takarar da suka hada da Ali Adjei Ibrahim, Felix Kumi Kwaku, Asante Oppong Alexander, da Adoma Hayford.[4] Ya taba rike mukamin mataimakin minista a ma’aikatar sa ido da tantancewa daga shekarar 2016 zuwa 2020, kuma a halin yanzu yana rike da mukamin mai ba da shawara kan fasaha a sakatariyar sa ido da tantancewa na ofishin shugaban kasa.[5]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheSabi Kirista ne. Yana da aure da yaro daya.
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Parliament of Ghana". www.parliament.gh. Retrieved 2020-02-08.
- ↑ UKGCC (2018-07-05). "HON. WILLIAM KWASI SABI". UK-Ghana Chamber of Commerce (in Turanci). Archived from the original on 2019-04-27. Retrieved 2020-02-08.
- ↑ "Ghana MPs - MP Details - Sabi, William Kwasi". www.ghanamps.com. Retrieved 2020-02-08.
- ↑ "Parliamentary Results - Dormaa EastConstituency". www.ghanaweb.com. Retrieved 2020-02-08.
- ↑ "Four deputy ministers vetted". ghananewsagency.org. Archived from the original on 2017-04-05. Retrieved 2020-02-08.