Wikipedia:National Board for Arabic and Islamic Studies

 

National Board for Arabic and Islamic Studies (NBAIS) (a cikin harshen Larabci المجلس الوطني للدراسات العربية والإسلامية) wata hukuma ce ta gwamnati da ke da alhakin tsarawa da aiwatar da manhajin karatun Larabci da na Musulunci a Najeriya . An kafa ta ne a shekarar 1960 a matsayin cibiya mai zaman kanta sannan ta zama sashe karkashin jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria, mai gudanar da ayyuka musamman a yankin arewacin Najeriya. A shekarar 2011, hukumar nada hurumin aiki a duk fadin kasar inda ta zama daya daga cikin hukumar jarrabawa a Najeriya.

Alhaji Sir, Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto ne ya kafa hukumar kula da larabci da addinin musulunci (NBAIS) a shekarar 1960. Daga nan sai ta zama sashe a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya a shekarar 1969. Hukumar ta sami sauye-sauye ta fuska daban-daban. Da farko ta kasance a matsayin hukumar reshen Arewacin Najeriya dauke da wasu Makarantu da Kwalejoji da ke karkashinta. A halin yanzu, tare da karramawa da amincewar Hukumar Kula da Ilimi ta Kasa (NCE) a taronta na 57 da ta gudanar a Sakkwato a watan Fabrairu, 2011, Hukumar a matsayin Hukumar Jarrabawa ta Kasa ta kunshi daukacin al’ummar kasa baki daya da manyan makarantu da kwalejoji sama da 900.

Hukumar kula da harshen Larabci da addinin Musulunci ta kasa na gudanar da jarrabawa a duk shekara ga manyan daliban da suka yi rajista da hukumar a fadin kasa. A halin yanzu, hukumar tana tsarawa da gudanar da jarrabawa daban-daban guda uku kowane zangon ilimi. Su ne:

  1. Jarrabawar shaidar kammala sakandare ta babbar makarantar Larabci da Islamiyya (SAISSCE)
  2. Jarrabawar Tahfeez ga daliban da suka kware wajen karatun Alqur'ani
  3. Kimiyya (don sauren fannoni)

Bayan fadada fagen ayyukan hukumar da ya shafi jihohin kasar nan 36 da suka hada da babban birnin tarayya Abuja, hukumar na fuskantar kalubale da dama. Wadannan kalubalen sun hada da amincewa da takardar shaidar da hukumar ta bayar. Yawancin cibiyoyin ilimi ciki har da wasu jami'o'in tarayya sun ki amincewa da takardar shaidar saboda wasu dalilai. Wani kalubale kuma shi ne zargin almubazzaranci da aka yiwa rajistarar cibiyar. A shekarar 2021 ne dai wata kafar yada labarai ta bayar da rahoton wani zarge-zargen da ake yi masa na karkatar da wasu makudan kudade na hukumar da hukumar ta musanta. Ta kuma zargi wasu manyan jami’an hukumar da daukar ‘yan uwa da abokan arziki aiki a hukumar.

Manazarta

gyara sashe