Wikipedia:Admin
Wikipedia nada yan sa kai na musamman da suke taimakawa wajen gyara da inganta Wikipedia ta Hausa. Wadannan yan sa kan kawai suna taimakawa wajen tabbatar da ci gaban Wikipedia amma hakan ba wai yana nufin cewar sunfi sauran editoci bane ko kuma za su iya yin abinda suka ga dama ba. Dukkan su dole subi ka'idojin Wikipedia kamar kowane sauran mai bada gudummuwa.
Ƙa'idojin zama Admin
gyara sashe- Ku rubuta saƙon neman Admin a Wikipedia:Ƙofar Al'umma
- Tattaunawa dole tayi aƙalla sati ɗaya (kwana bakwai)
- Dole ne a samu cikakken goyon baya daga masu tattaunawa
- Wajibi ne admin yabi ƙa'idojin Wikipedia wajen amafani da tools na admin