Ammarpad
Ya yi rajista 16 ga Afirilu, 2015
![]() Domin haɓaka wannan manhaja, na shirya taron Hausa Wikipedia a Kano a shekarar 2018 wanda shine taron farko akan hakan a duk faɗin Arewacin Najeriya. Daga nan an shirya wasu tarukka ba adadi a wurare daban daban na sassan Najeriya. Idan kai bahaushe ne ko ke bahaushiya ce, ina gayyatar ku mu inganta wannan rumbun ilimin. Idan kuna buƙatar ƙarin bayani, shawara ko ƙarin haske a kan Hausa Wikipedia ko yadda zaku bada gudummuwa, zaku iya tambaya ta a nan ko kuma ku tura man saƙon email ta ammar Har ila yau, ina kuma da wani account wanda yake aiki da kanshi (wato robot), amma fa yana jin Hausa kamar jakin Kano. Zaku iya ganin ayyukan shi a nan: AmmarBot. |
|