Victoria Kwakwa
Victoria Kwakwa kwararriya ce kuma masaniyar tattalin arziƙin Ghana kuma ta yi aiki a matsayin mataimakiyar shugaban Bankin Duniya na Gabashin Asiya da Pacific tsakanin shekarun Afrilu 2016 da Agusta 2021.[1][2] Ita ce darekta ta bankin duniya a Vietnam kafin matsayinta na yanzu.[3]
Victoria Kwakwa | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Ghana, |
ƙasa | Ghana |
Karatu | |
Makaranta |
Queen's University (en) Doctor of Philosophy (en) , Master of Arts (en) University of Ghana University of Ghana Bachelor of Arts (en) : ikonomi Queen's University (en) |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | Mai tattala arziki |
Mahalarcin
|
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheTa sami digiri na biyu a fannin tattalin arziki da kididdiga daga Jami'ar Ghana, Legon. Daga baya ta halarci Jami'ar Queens da ke birnin Kingston na ƙasar Canada don samun digirin digirgir a fannin tattalin arziki tare da ƙwarewa a fannin kasuwanci da hada-hadar kuɗi da ka'idar kuɗi.[4]
Sana'a
gyara sasheTa fara aikinta a matsayin matashiya masaniyar tattalin arziki tare da Bankin Duniya (WB) a cikin shekarar 1989.[5] A matsayinta na Shugabar yankin Gabashin Asiya na Pacific, Kwakwa ita ce manajar kai tsaye na Rodrigo Chaves wanda a ƙarshe aka tilasta masa yin murabus daga WB a karshen shekarar 2019 bayan korafe-korafe da dama na lalata da cin zarafi. Bincike na cikin gida ya kai ga kiransa zuwa Washington kuma an rage shi. Chaves ya kasance darektar WB na ƙasar Indonesiya 2013-2019 wanda daga cikin korafe-korafe da yawa suka taso. Kwakwa bata ɗauki mataki ba. Daga baya Chaves ya zama Ministan Kuɗi na Costa Rica.[6][7]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Victoria Kwakwa World Bank Vice President for East Asia and Pacific Archives". Vanuatu Independent (in Turanci). Retrieved 2018-05-30.
- ↑ "Victoria Kwakwa". World Bank. Retrieved 23 September 2021.
- ↑ Ayitey, Charles. "Ghanaian Victoria Kwakwa gets top World Bank appointment". Yen.com.gh - Ghana news. (in Turanci). Retrieved 2018-05-30.[permanent dead link]
- ↑ "The full text of Nigeria's President Muhammadu Buhari's Democracy Day Speech - Ventures Africa". Ventures Africa (in Turanci). 2018-05-29. Retrieved 2018-05-30.
- ↑ "Victoria Kwakwa, World Bank Group/The: Profile & Biography". Bloomberg (in Turanci). Retrieved 2018-05-30.
- ↑ Pérez, Santiago (18 October 2021). "WSJ News Exclusive | World Bank Mishandled Sexual-Harassment Claims, Internal Tribunal Says". Wall Street Journal.
- ↑ "President Jokowi Hosts World Bank President". Sekretariat Kabinet Republik Indonesia. 26 July 2017.