Uzziel Ndagijimana
Uzziel Ndagijimana masanin tattalin arziki ne dan kasar Rwanda wanda ke rike da muƙamin ministan kuɗi da tsare-tsare a gwamnatin shugaba Paul Kagame tun daga shekarar 2018.[1][2]
Uzziel Ndagijimana | |||
---|---|---|---|
6 ga Afirilu, 2018 - 15 ga Augusta, 2024 ← Claver Gatete (en) | |||
Rayuwa | |||
ƙasa | Ruwanda | ||
Karatu | |||
Makaranta |
Jami'ar Rwanda University of Warsaw (en) Doctor of Philosophy (en) : ikonomi | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Mai tattala arziki, malamin jami'a da Malami | ||
Mahalarcin
|
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheNdagijimana yana da digirin digirgir a (PhD, Economics), 1998 daga Jami'ar Warsaw da MSc. a fannin Ilimin tattalin arziki daga Warsaw School of Economics.Economics]].[3]
Sana'a
gyara sasheNdagijimana ya fara aikinsa a matsayin malami a tsangayar tattalin arziki, kimiyyar zamantakewa, da gudanarwa a jami'ar ƙasa ta Rwanda a shekarar 1999. A shekara ta 2002, ya koma shugabanci na gwamnatin Rwanda.[4]
Ndagijimana ya zama shugaban Makarantar Kuɗi da Banki a Kigali, Rwanda, daga shekarun 2002 zuwa 2007 bayan haka ya zama mataimakin shugaban jami'ar kasar Rwanda daga shekarun 2007 zuwa 2011.[4][5]
Ndagijimana shi ne Babban Sakatare na Ma'aikatar Lafiya, Jamhuriyar Ruwanda, daga watan Mayu 2011 zuwa watan Yuli 2014. Ya kuma kasance Ƙaramin Minista mai kula da Tsare-Tsare Tattalin Arziki a Ma'aikatar Kuɗi da Tsare Tattalin Arziki (MINECOFIN).[2]
A yayin babban taron shekara-shekara na bankin Afreximbank a Abuja don tunawa da cika shekaru 25 da kafuwa, ministar kuɗin Najeriya Kemi Adeosun ta gaji Ndagijimana a matsayin shugaban hukumar bankin.[6]
A ranar 7 ga watan Afrilu, 2018, Shugaba Paul Kagame ya naɗa Ndagijimana a matsayin ministan kuɗi da tsare-tsare na Ruwanda.[1] Ndagijimana ya kuma taɓa zama shugaban kwamitin ba da shawara kan tattalin arziki na shugaban ƙasar Rwanda.[4]
Sauran ayyukan
gyara sashe- Bankin Raya Afirka (AfDB), tsohon memba na kwamitin gwamnoni (tun 2018) [7]
- Bankin Raya Gabashin Afirka (EADB), tsohon memba na majalisar gudanarwa (tun 2018) [8]
- Asusun Ba da Lamuni na Duniya (IMF), tsohon memba na kwamitin gwamnoni (tun 2018) [9]
- Bankin Duniya, Tsohon Jami'in Hukumar Gwamnoni (tun 2018) [10]
- Jami'ar Ƙasa ta Ruwanda, Memba na Kwamitin Gudanarwa
- Babban bankin ƙasar Rwanda, memba na kwamitin gudanarwa
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 "Rwanda's president names new finance minister in reshuffle". Reuters. Archived from the original on 2022-02-26. Retrieved 2018-07-23.
- ↑ 2.0 2.1 "Minister Uzziel Ndagijimana takes over at MINECOFIN, calls for continued collaboration". www.minecofin.gov.rw (in Turanci). Archived from the original on 2018-07-23. Retrieved 2018-07-23.
- ↑ "Uzziel Ngagijimana". IGC (in Turanci). Retrieved 2019-12-26.
- ↑ 4.0 4.1 4.2 "Uzziel Ndagijimana". World Bank Live (in Turanci). 2018-04-12. Retrieved 2018-07-23.
- ↑ "Uzziel Ngagijimana - IGC". IGC (in Turanci). Retrieved 2018-07-23.
- ↑ "Kemi Adeosun elected Afreximbank board chairperson | TODAY.NG". TODAY.NG (in Turanci). 2018-07-14. Retrieved 2018-07-26.
- ↑ 2019 Annual Report African Development Bank (AfDB).
- ↑ Governing Council East African Development Bank (EADB).
- ↑ Members International Monetary Fund (IMF).
- ↑ Board of Governors World Bank.