Ubomiri
Gari a Nijeriya
Ubomiri gari ne da ke cikin Mbaitoli na jihar Imo da ke kusa da Owerri babban birnin jihar Imo a kudu maso gabashin Najeriya.
Ubomiri | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Yawan mutane | ||||
Harshen gwamnati | Harshen, Ibo | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Sabuwar Kasuwar Duniya ta Jihar Imo, wacce aka fi sani da Ahia Rochas, tana Ubomiri.[1]
Geography
gyara sasheUbomiri tsohuwar masarauta ce da ta ƙunshi kauyuka tara da suka haɗa da: Egbeada, Amauburu, Umuabali, Obookpo, Umuocha, Ohuba, Ohum, Ahama da Umuojinaka.
A halin yanzu, Ubomiri ya ƙunshi al'ummomi masu cin gashin kansu guda uku:
- Al'ummar Amawuihe mai cin gashin kansa, wacce ta kunshi kauyukan Ahama Ohum Umuocha da Ohuba. Sarki mai mulki shine Eze Clifford R. Amadi mai Uhie 1 na Amawuihe.
- Ishi Ubomiri mai cin gashin kansa, wanda ya kunshi kauyukan Obokpo Umuabali Amauburu da Umuojinaka. Sarkin da ke mulki shi ne Eze George Eke Ishi 1 na Ishi Ubomiri.
- Egbeada Autonomous Community, wanda ya ƙunshi ƙauyen Egbeada. Sarki mai mulki shine Eze Edward The Ada 1 of Egbead.
Ubomiri na kewaye da garuruwa da suka haɗa da; Akwakuma, Ifakala, Irete, Ohii, ogbaku, Amakohia da Mbieri da Nwaorieubi, hedkwatar karamar hukumar Mbaitoli.
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Nwaorieubi as an emerging urban centre in mbaitoli l.G.A,1976-2015". Project Gist International (in Turanci). Archived from the original on 2022-07-02. Retrieved 2022-07-08.