Tshotlego Morama, an haife ta a Lethakane a cikin shekarar 1987,[1] 'yar wasan tseren Paralympic ce ta Botswana.

Tshotlego Morama
Rayuwa
Haihuwa Letlhakane (en) Fassara, 2 ga Faburairu, 1987 (37 shekaru)
ƙasa Botswana
Sana'a
Sana'a Dan wasan tsalle-tsalle
Athletics
Records
Specialty Criterion Data M
Personal marks
Specialty Place Data M
 

Ta wakilci Botswana, a gasar wasannin nakasassu ta bazara ta shekarar 2004 a Athens, ta lashe zinare a tseren gudun mita 400 na mata a rukunin nakasassu na T46, inda ta kafa sabon tarihin duniya a cikin wannan tsari, tare da lokacin 55.99. [2][3] Ta kasance 'yar wasa tilo da ta taɓa wakiltar Botswana a gasar Paralympics.[3]

Morama ta kuma lashe zinare a gasar All-African Games na shekarar 2007, wacce ta kafa sabon tarihi a Afirka a tseren mita 200 na mata.[4]

Morama ta kamata ya sake wakiltar Botswana a gasar wasannin nakasassu ta bazara na shekarar 2008 a Beijing,[5] amma a ƙarshe bata shiga gasar ba,[3] ta janye kafin gasar saboda rauni.[6]

Manazarta

gyara sashe
  1. "Morama sets sights at next Olympics" Archived 2004-11-09 at the Wayback Machine, Botswana Press Agency, October 5, 2004
  2. "IWAS website". Archived from the original on 2012-02-10. Retrieved 2024-03-20.
  3. 3.0 3.1 3.2 Botswana at the Paralympics, International Paralympic Committee
  4. "No Chance For Karate At BNSC Awards?"[permanent dead link], The Botswana Gazette
  5. "Tshotlego for Paralympics" Archived 2011-08-13 at the Wayback Machine, Dailynews, Botswana government website, July 14, 2008
  6. "Botswna locked out of Paralympics" Archived 2012-11-30 at Archive.today, Mmegi, 5 September 2008