Toyin Afolayan
Toyin Afolayan (an haife ta a 24 Satumban Shekarar 1959) wanda aka fi sani da Lola Idije yar fim din Najeriya ce kuma goggo ce ga fitaccen jarumin fina-finan Najeriya Kunle Afolayan. Ta samu daukaka ne bayan ta fito a matsayin Madam Adisa a fim din 1995 mai taken Deadly Affair .[1]
Toyin Afolayan | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Toyin Afolayan |
Haihuwa | Kwara, 24 Satumba 1959 (65 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Yarbanci |
Ƴan uwa | |
Ƴan uwa |
view
|
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Yarbanci |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
IMDb | nm2400161 |
Toyin Afolayan an san shi da wanda ya fara kirkirar maganganun yanar gizo Soro Soke da Pele My Dear. Soro Soke Were kalma ce da masu zanga-zangar #EndSars suke amfani da ita a Najeriya don neman Gwamnati ta yi Magana da Murya a kan wuce gona da iri na rundunar 'yan sanda ta SARS a kasar.
Tarihin Rayuwa
gyara sasheToyin Afolayan dan asalin Agbamu ne, jihar Kwara a kudu maso yammacin Najeriya.[1] Ita ce kani ga Adeyemi Afolayan (aka Ade Love)[1] da ’ya’yansa, ’yan fim na Najeriya Kunle Afolayan, Gabriel Afolayan, Aremu Afolayan da Moji Afolayan. Toyin ya fara wasan kwaikwayo a shekarun 80s saboda tasirin Ade Love.[2] Ta ci gaba da taka rawa a Nollywood har zuwa yau, inda ta fito da yawa a fina-finan Yarbanci.
Tsohuwar jarumar ta kasance a cikin masana'antar fina-finai kusan shekaru 30 a cikinta inda ta yi suna a shekarar 1995 saboda rawar da ta taka a matsayin Mama Adisa a cikin fim din 'Deadly Affair'.[3]
Rayuwa ta sirri
gyara sasheToyin Afolayan bazawara ce,[4] uwa ce mai ‘ya’ya mata uku da kaka.[5] Danta tilo ya rasu tun tana karama.[1] An nada Toyin Afolayan kwanan nan a matsayin jakadan Boalas Homes and Gardens.[6]
Filmography zaba
gyara sashe- Glimpse (2020)[7]
- Arojinle (2018)[8]
- Ojuloge Obirin (2017)[9]
- Irapada (2006)
- Deadly Affair (1995) as Madam Adisa
- Ayomida (2003) as Judge
- Botife (2004) as Ajibike
- Osunwon Eda (2006)
- Idunnu mi (2007)
- Taiwo Taiwo (2008) as Egbon Joke
- Elewon (2009) as Iya Aliah
- Olokiki oru: The Midnight Sensation (2019) as Olori
- Anikulapo (2022) as Oyo Chief
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 http://encomium.ng/at-my-age-remarrying-shouldnt-be-a-priority-again-lola-idije/
- ↑ https://punchng.com/10-matriarchs-of-nigerian-movie-industry/
- ↑ https://guardian.ng/art/toyin-afolayan-gets-baolas-homes-and-gardens-ambassadorial-role/
- ↑ http://encomium.ng/god-has-been-my-pillar-all-along-toyin-afolayan-lola-idije-on-life-55/
- ↑ https://motherhoodinstyle.net/2020/03/02/veteran-actress-toyin-afolayan-lola-idije-tells-children-prevented-getting-married-husbands-death/
- ↑ https://guardian.ng/art/toyin-afolayan-gets-baolas-homes-and-gardens-ambassadorial-role/
- ↑ BellaNaija.com (2020-08-10). "There's A New Teaser for Biodun Stephen's Film "Glimpse" starring Bisola Ayieola & Lola Idije". BellaNaija (in Turanci). Retrieved 2021-12-04.
- ↑ "Arojinle". irokotv.com (in Turanci). Irokotv. 2018. Archived from the original on December 4, 2021. Retrieved 24 May 2023.
- ↑ Tv, Bn (2017-09-13). "#BNMovieFeature: WATCH Bobrisky, Lola Idije, Tayo Sobola in "Ojuloge Obirin"". BellaNaija (in Turanci). Retrieved 2021-12-04.