Theo Walcott An haifeshi a ranar goma sha shida 16 shekarar alif dubu daya da dari tara da tamanin da tara 1989. Tsohon dan wasan ƙwallon ƙafa ne dan asalin kasar Ingila. A shekarar alif dubu biyu da shida 2006 ya wakilci kasar Ingila a fasr cin kofin duniya. Haka zalika ya wakilci kasar tashi a gasar Euro wanda aka buga a shekarar alif dubu biyu da goma sha biyu 2016 inda dan wasan ya buga wasanni guda arba'in da bakwai 47 inda ya samu nasarar jefa kwallaye guda takwas 8 a raga.

Walcott kaya ne na kungiyar kwallon kafa ta Southampton academy, sannan kuma ya jona kungiyar kwallon kafar Southamptom kafin ya koma ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Arsenal akan jumillar kudi £5m ashekara ta alif dubu biyu da shida 2006. Saboda gudunsa da kuma iya tafiya da kwallo da kuma takonsa, mai bashi horo kuma babban koci wato Arsene Wenger ya maidashi dan wasan gefe a yawancin rayuwar kwallon shi. Dan wasan ya buga wasa a matsayin dan wasan gaba na tsakiya tun shekara ta alif dubu biyu da goma sha ukku 2013 zuwa da goma sha hudu 2014 inda da yake yana cikin wadanda suka fi kowa zura kwallo a cikin raga inda ya samu nasarar jefa kwallaye sama da dari 100 a raga a kungiyar kwallon kafa ta Arsenal din.

A ranar talatin 30 ga watan Mayu shekarar alif dubu biyu da shida 2006. Walcott ya zama dan wasa mai karancin shekaru a ƙasar Ingila inda yake da shekaru goma sha bakwai 17 da kuma kwanaki guda saba'in da biyar. A watan Disamba, dan wasan ya samu nasarar lashe gwarzon dan wasa mafi karancin shekaru inda yaci kyautar BBC young sport personally of the year. A ranarvshida 6 ga watan September shekarar alif dubu biyu da takwas 2008 ya fara buga gasar shi ta farko a matsayin kwararren dan wasa a gasar tsallakewa cin kofin duniya a wasan da suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta kasar Andorra. Wasa na gaba kuma suka fafata da kungiyar kwallon kafa ta Croatia a ranar goma 10 ga watan September. Dan wasan ya kasance dan wasa mai karancin shekaru a tarihin kasar Ingila da ya zura kwallaye guda ukku ringis a wasa daya.


Rayuwar baya

gyara sashe

An haifi dan wasan inda baban sa ya kasance bakine dan kasar jamaica. Mamar dan wasan kuma ta kasance fara ce kuma baturiya yar kasar Ingila. An haifeshi a yankin Stanmore dake Landan amma ya girma ne a Compton Berkshire yaje cocin Compton a makarantar firamare dake ƙasar Ingila da kuma makarantar downs. Ya tashi ne a matsayin mai goyon bayan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool saboda babanshi yana daya daga cikin magoya bayan kungiyar kwallon kafar ta Liverpool. Lokacin da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea suka tambaye shi ya zama yaron dauko kwallo, anan ya samu damar haduwa da yan kwallon da yake muradin haduwa dasu yan Liverpool.

Manazarta

gyara sashe

https://en.wikipedia.org/wiki/Theo_Walcott