Thelma Awori
Thelma Awori farfesa ce 'yar Uganda, tsohuwar Mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya, kuma mai kare hakkin mata. An haife ta a ranar 25 ga watan Maris, 1943, a Monrovia, Laberiya kuma ta zo Uganda a shekarar 1965.[1] Tsohuwar 'yar majalisar jama'ar Uganda diehard ce, wacce ta sauya sheka zuwa Harkar.[2] Ita mace ce mai kare hakkin mata Afirka wacce ta yi imani da adalci ga mata da ingancin ra'ayin mata. Cikin ɓacin rai ta sami yawaitar zalunci na cikin gida saboda addini da zamantakewa.[3][4]
Thelma Awori | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 25 ga Maris, 1943 (81 shekaru) |
ƙasa |
Uganda Laberiya |
Ƴan uwa | |
Abokiyar zama | Aggrey Awori (en) |
Karatu | |
Harsuna | Turanci |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa, Malami da gwagwarmaya |
Ilimi
gyara sasheTa yi karatu a Jami'ar Harvard yayin da ta samu digiri na farko na Arts cum laude Social Relations & Cultural Anthropology. A Jami'ar California a Berkeley, ta sami Masters na Ilimin a Adult Education & Humanistic Psychology.[5] Ta sami digiri na uku a cikin shekarar 2006 daga Jami'ar Columbia a birnin New York.[1][5]
Gwanintar aiki
gyara sasheTana zaune a Uganda kuma tana aiki a faɗin nahiyar Afirka. Baliga ce mai koyar da tarbiyya da tada hankalin mutane a fagen siyasa game da jinsi da rashin adalci na tattalin arziki.[3] Thelma ƙwararriyar malama ce. Ta yi aiki a matsayin mataimakiyar Darakta a UNIFEM tun a shekarar 1990. An kuma ɗauke ta a matsayin shugabar sashen Afirka, UNIFEM, New York. Ta yi aiki a matsayin mai ba da shawara a UNIFEM, ILCO na Netherlands, Asusun Yara na Majalisar Ɗinkin Duniya, da Hukumar Raya Ƙasa ta Amurka, tun a shekarar 1981.
Thelma ta kuma yi aiki a matsayin Babbar Sakatariya, Hukumar Ilimin Sadarwa, Ƙungiyar Duniya don Sadarwar Kirista, London, 1977-1981. Daga shekarun 1973 zuwa 1977, ta yi aiki a matsayin Malama a Kwalejin Adult and Distance Education a Jami'ar Nairobi, Kenya. Tsakanin, shekarun 1965-1972. Ta kasance Babbar Jagora a Cibiyar Ci gaba Jami'ar Makerere, Uganda tana koyar da ilimin zamantakewa.[1] Ta kammala wa'adin shekaru biyu a matsayin mataimakiyar Sakatare-Janar na Majalisar Ɗinkin Duniya.[6]
Ita ce babbar darektar Cibiyar Canjin Zaman Jama'a (IST), kuma tana aiki a matsayin mai ba da shawara ga gwamnatin Laberiya a Uganda. Ta rinjayi manufofi da ayyuka a faɗin nahiyar. Ta yi aiki a matsayin mataimakiyar Sakatare Janar mai kula da Ofishin UNDP na Afirka da ke New York.[7][8][9] Thelma Awori ita ce shugabar hukumar kula da jagoranci ta Afirka.[7] Ita ce Honorary consul ta Laberiya a Uganda.[1][10]
Tsohuwar mataimakiyar sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya ce kuma shugabar ofishin yankin Afirka na shirin ci gaban Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP).[11][12] Ta yi hidimar Majalisar Ɗinkin Duniya na tsawon shekaru 12, a matsayin mataimakiyar darakta na UNIFEM kuma a matsayin mai kula da tsarin Majalisar Dinkin Duniya a Zimbabwe.[5] Daga shekarar 1965, ta kasance mai taka rawar gani a gwagwarmayar adalci na matan Uganda na samar da daidaito tsakanin jinsi kuma shi ya sa a ranar 8 ga watan Maris 2018, ta kasance daya daga cikin mata 10 da aka amince da su kuma aka karrama ta saboda sanya Uganda alfahari a fannoni daban-daban na kokarin ɗan Adam a ƙasar.[1]
Ita ce Shugabar Kafa kuma Mataimakiya Shugaban, Asusun Mata na Kasuwa Mai Dorewa, Laberiya a da (Asusun Mata na Kasuwar Sirleaf ) wanda kai tsaye da kuma a kaikaice ta ba wa matan kasuwa sama da 15,000 a Laberiya.[5]
Sauran nauye-nauye
gyara sasheTana cikin Membobin Ƙungiyar Afirka da Karatu da Ilimin Manya, Nairobi, da Ƙungiyar Amirka da Horo da Ci gaba. a Kwamitin Gudanarwa na Kungiyar Shugabancin Mata ta Afirka inda take tsara shirye-shiryen da ke karfafa mata a harkar noma da tallafa wa mata masu sayar da kayayyaki a faɗin nahiyar.[8]
Bayanan sirri
gyara sasheTa yi aure da Aggrey Awori wanda shi ne Ministan Watsa Labarai da Fasahar Sadarwa a Majalisar Dokokin Uganda daga ranar 16 ga watan Fabrairu 2009 zuwa ranar 27 ga watan Mayu 2011.[1] Aggrey Awori da Thelma Awori sun haɗu a Jami'ar Harvard, Amurka, a cikin shekarun 1960 lokacin da suke ɗalibai a Jami'ar Harvard.[2]
Duba kuma
gyara sashe- Aggrey Awori
- Margaret C. Snyder
- Angelina Wapakhabulo
- Pumla Kisosonkole
Manazarta
gyara sashe- ↑ 1.0 1.1 1.2 1.3 1.4 1.5 "In honour of 10 Ugandan women of foreign origin". Daily Monitor (in Turanci). 29 January 2021. Retrieved 2021-03-20.
- ↑ 2.0 2.1 "Museveni swears in new ministers". 2015-04-13. Archived from the original on 2015-04-13. Retrieved 2021-03-20.
- ↑ 3.0 3.1 "Thelma Awori » African Feminist Forum". African Feminist Forum (in Turanci). 2016-03-18. Retrieved 2021-03-20.
- ↑ "Women's Day public dialogue – Men urged to treat women as allies not subordinates | News@CHUSS". chuss.mak.ac.ug. Retrieved 2021-03-20.
- ↑ 5.0 5.1 5.2 5.3 Technology, University Outreach and Engagement-Communication and Information. "African Women Post Independence: Economic Empowerment, Peace, and Security". gess.msu.edu (in Turanci). Retrieved 2021-04-07.
- ↑ "Election Special". Harvard Magazine (in Turanci). 2000-11-01. Retrieved 2021-03-20.
- ↑ 7.0 7.1 "Board". aflinstitute.net. Archived from the original on 2021-04-23. Retrieved 2021-03-20.
- ↑ 8.0 8.1 "Amujae Leaders join an insightful session with Ellen Johnson Sirleaf and Amujae Coaches Vera Songwe, Zainab Bangura, and Thelma Awori". EJS Center (in Turanci). 2020-12-17. Archived from the original on 2023-06-03. Retrieved 2021-03-20.
- ↑ "Treaty bodies Search". tbinternet.ohchr.org. Retrieved 2021-03-20.
- ↑ "Liberia Consulate in Kampala". www.consulate-info.com. Retrieved 2021-03-20.
- ↑ Charlick, Robert B. (2000). "Comprehending and Mastering African Conflicts: The Search for Sustainable Peace and Good Governance (review)". Africa Today. 47 (2): 171–173. doi:10.1353/at.2000.0031. ISSN 1527-1978. S2CID 143399366.
- ↑ Thelma, Awori; Director, UNDP. Europe and the Commonwealth of Independent States. Assistant Administrator and Regional (1999-07-20). "Record #403814". United Nations Digital Library System (in Turanci).