Thatayaone Mothuba
Thatayaone Mothuba (an haife shi a ranar 5 ga watan Mayun 1978) ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na Botswana, wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron baya a ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Nico United tun 2003.[1] An fara kiran Mothuba zuwa tawagar kwallon kafa ta Botswana a shekarar 2001, kuma yayi nasarar ciwa kasarsa wasanni biyu a shekarar 2002.[ana buƙatar hujja]
Thatayaone Mothuba | |||||||||||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Gaborone, 5 Mayu 1978 (46 shekaru) | ||||||||||||||||||||||||||||||
ƙasa | Botswana | ||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||||||||||
| |||||||||||||||||||||||||||||||
Muƙami ko ƙwarewa | Mai buga baya |
Sana'a
gyara sasheAn haifi Thatayone Mothuba a ranar 5 ga watan Mayun 1978. Ya buga wa Botswana wasa a kasa da shekara 17,20,23, babbar tawagar kasar kuma yana cikin tawagar da ta lashe gasar Botswana 4 a lokacin da ya zura kwallo a ragar Namibiya. Kwararren mai tsaron baya ne wanda yake da hikimar kwatar kwallo. Ya lashe gasar zakarun Afrika tare da tsohuwar kungiyar kwallon kafa ta Notwane.[2] Yana cikin tawagar da ta buga kunnen doki babu ci a gasar COSAFA castle Cup a filin wasa na kasar Gaborone. A halin yanzu shi mataimakin koci ne a kulob ɗin Nico United a Selebi Phikwe, ya yi aiki tare da irinsu tsohon dan wasan kasar Zimbabwe Madinda Ndlovu, Luke Masumera, Paul Gundani.[ana buƙatar hujja]