Barka da zuwa!

gyara sashe

Ni Robot ne ba mutum ba.

 
Hausa Wikipedia na buƙatar gudummuwarku domin ta bunƙasa!

Barka da zuwa Hausa Wikipedia, Pharouqenr! Mun ji daɗin gudummuwarku. Kuma muna fatan zaku tsaya ku ci gaba da bada gudummuwa. Anan ƙasa ga wasu shafuka da zasu taimaka wajen fahimtar Hausa Wikipedia da yadda ake gyara ta:

Zaku iya yin sayinin rubutunku idan kuna akan shafukan tattaunawa ta hanyar alamar tilde guda huɗu, kamar haka (~~~~); yin hakan, zaisa sunanku da cikkaken kwanan wata. In kana buƙatar wani taimako, ku duba Wikipedia:Tutorial. Na gode. AmmarBot (talk) 21:27, 25 Nuwamba, 2023 (UTC)Reply

Barka da Kokari

gyara sashe

@Pharouqenr....barka da kokari da kuma jajircewarka wurin tabbatar da ailimi a wikipedia ta hausaSaifullahi AS (talk) 20:09, 18 Mayu 2024 (UTC)Reply

Gyara

gyara sashe

Brk da wannan lokaci @Pharouqenr. Na ga kana ta editing ko gyara hakan yayi. Amman mu riƙa sanin ya kamata wurin gyaran na mu. Ma'ana mu riƙa mai ma'ana sosai. Misali kaga ana rubuta shekarar da lambobin (1999), ka kuma sai ka goge ko kara rubuta wannan sunan shekara da kalmomi. Wanda hakan kuskure ne kasancewar duk wani bahaushe da yaga an rubuta 1999 to ya san mi aka saka ba kukatar kuma a sake rubuta shekarar da kalmomi. Idan da ba'a saka da lambobin ba kai kuma ka saka da kalmomi hakan ba wani abu bane. Ina fatan za mu kula!. Nagode. BnHamid (talk) 06:30, 1 ga Yuni, 2024 (UTC)Reply

Gyara

gyara sashe

Aslm @Pharouqenr brk da aiki. Naga kana ta ƙirƙirar makaloli hakan na da kyau. Sai dai dukkan Makalolin da ka kirkiro suna bukatar gyara sosai Misali kamar wannan makalar DA KA KIRKIRO ta na bukatar gyara. Kuma na bibiyi gyararrakinka hakan na bukatar ka san ya ake gyara a Wikipedia.

Ina mai kara jan hankali da ka je ka karanta yadda ake kirkiro makala gami da yadda zaka saka mata Manazart/Reference sannan ka je ka gyara makalolin idan ba ka gyara ba za'a goge su kuma za'a dau mataki akan an faɗa maka kuskure amman baka gyara ba. An baka dama kaje ka karanta gami da tambaya don ka iya gyara mai ma'ana, dama kirkirar Makala. BnHamid (talk) 08:45, 11 ga Yuni, 2024 (UTC)Reply

@bnhamid kayi man magana akan gyararraki Nagode da hakan. Sannan inaso fada man mukalolin da suke buƙatar gyara domin in gyara. Pharouqenr (talk) 09:27, 11 ga Yuni, 2024 (UTC)Reply
Gaba-daya dukkan malakar da ka kirkiro, suna bukatar gyara, ka SHIGA WANNAN LINK don ganin dukkanin makalar da ka kirkiro.
Ina so ka fahimci cewa mu dukkan mu nan Hausawa ne mun san mi ake kira da Gyara Hakazalika idan muna karanta makala za mu fahimci idan mai INGANCI ce ko AKASI bugu da kari ana rubuta makalar nan da yaren HAUSA bawai da wani YARE ba. Don haka idan makala zata KARANTU mun sani haka idan bata da kyau mun sani. Ba wai da wani yare ake gyaran makalar Hausa ba.
Kasancewar mun amince zamu bayar da gudummawa akan aikin sa kai, ba shi ne lamunin cewa zamu watsar da dokar da ta kafa wannan aikin na sa kai da za muyi ba. Ina mai kara shawartarka da ka karanta wannan SHAFIN GABADAYA. A karshe ina mai sanar da mu abin nan da muke yi aikin sa kai me ba WAJIBI ba, Amman tunda mun yarda za muyi to fa TILAS mu bi ka'idojin da sharudan da muka amince kafin mu bayar da gudummawa kasancewar HAUSA WIKIPEDIA ta na da dokokin da bamu muka kafa su ba, ita kanta Hausa Wikipedia ba ita ta kafa dokokin ba face GIDAUNIYAR WIKIPEDIA ta duniya bakiɗaya. Nagode. BnHamid (talk) 09:51, 11 ga Yuni, 2024 (UTC)Reply
Nagode sosai @bnhamid zan gyara sosai musamman a wajan sanya manazarta saidai a cikin mukalar ina fassara abinda na gani ne a cikin Mukalar ta turanci sai in fassara ta zuwa harshen hausa. Banda wannan shi minene ya kamata in gyara? Nagode Pharouqenr (talk) 10:15, 11 ga Yuni, 2024 (UTC)Reply
@bnhamid brk d aiki, duk wasu ka'idoji da ake bi ana yin gyara acikin fai fan daka turo man nabishi, saidai har yanzu ban san mi akeso in gyara ba. Sannan mukala ce kawai nake fassarawa in sanya mata Manazarta da duk abinda ake bukata, to minene abun kuskure anan?. Inma anyi kuskure to daga English Wikipedia ne saboda duk wani information daga can yake namu kawai fassarawa. Nagode Pharouqenr (talk) 03:50, 18 ga Yuni, 2024 (UTC)Reply

Request for unblocking my account

gyara sashe

User:Gwanki naga bnhamid ya sanya kayi blocking dina daga yin gyara, amma inaso a matsayin ka na Admin mai adalci ka duba muƙalolin dana ƙirƙira kaga idan akwai wasu ƙa'idoji da na karya. Nagode ina bukatar adalci daga wurinka. Pharouqenr (talk) 09:22, 18 ga Yuni, 2024 (UTC)Reply

@Pharouqenr a ina kaga nace yayi blocking na ka ?!!!. Ya kamata kasan irin maganar da yakamata kana faɗa. Kuma da kake maganar ka'idoji da ka karya kusan dukkan gyarnka da makalolin ka basu da Inganci Asali ma baka fahimci Micece Wikipedia ba har yanzu. Na baka misalai Kaje ka diba MISALI MAKALAR JAMI'AR JOS ka karanta sannan ka karanta makala daya taka.
Rashin ingancin aikin ka ya haɗa da;
Rashin tsara rubutu
Rashin gyara mai ma'ana
Ba ka bin ka'idojin Rubutun Hausa
Ba'a iya karanta section daya na makalar ka lafiya lau ba tare da tarin kura-kurai ba.
Etc...
Dayan babban kuskure ka kuma shine da idan an kyale kana ta kuskure kana tunani ai dadai kake yi.
Menene ma'anar makalar da bata karantuwa ? Na faɗa maka WIKIPEDIA HAUSA da Hausa ake rubutata ba wanda zai karanta abinda aka rubuta da Hausa kuma bahaushe me amma ya kasa gane Inganci rubutun abinda aka karanta.
Ya kamata mu riƙa fada ma. Ka jaraba yin gyara a WIKIPEDIA TA TURANCI ZAKA FAHIMCI DIGO DAYA IDAN KA SAKA fiye da daya BA DAIDAI BA HAR BLOCKING PERMANENTLY ZA'A IYA. BnHamid (talk) 09:56, 18 ga Yuni, 2024 (UTC)Reply