Barka da zuwa!

gyara sashe

Ni Robot ne ba mutum ba.

 
Hausa Wikipedia na buƙatar gudummuwarku domin ta bunƙasa!

Barka da zuwa Hausa Wikipedia, Muhammad Musa Tika! Mun ji daɗin gudummuwarku. Kuma muna fatan zaku tsaya ku ci gaba da bada gudummuwa. Anan ƙasa ga wasu shafuka da zasu taimaka wajen fahimtar Hausa Wikipedia da yadda ake gyara ta:

Zaku iya yin sayinin rubutunku idan kuna akan shafukan tattaunawa ta hanyar alamar tilde guda huɗu, kamar haka (~~~~); yin hakan, zaisa sunanku da cikkaken kwanan wata. In kana buƙatar wani taimako, ku duba Wikipedia:Tutorial. Na gode. AmmarBot (talk) 00:02, 12 Disamba 2021 (UTC)Reply

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

Tarihin rayuwar Dakta Idriss Yusuf Madaki(Galadiman Dozi, Zarma kuran masarautar Gudi)

An haifi Dakta Idriss Yusuf Madaki a shekara ta alif dubu daya da dari tara da saba'in 1970 a garin Balde dake karamar hukumar Fika a jihar Yobe dake shiyyar arewa maso gabashin Nijeriya, izuwa yanzu yana da mata da kuma yara.

              MATAKAN FARKO NA KARATU.

Dakta ya fara karatu daga matakin firamare a shekara ta 1978 zuwa shekara ta 1984 a makaranta Balde primary school dake karamar hukumar Fika, Bayan karbar shaidar kammalawa Dakta ya kara gaba izuwa matakin karamar sakadire daga shekara ta 1984 zuwa 1986 a makaratar GSS Nangere dake karamar hukumar Nangere a jihar yobe, daga nan sai makarantar GSS Jakusko dake karamar hukumar Jaskusko a jihar yobe daga shekara ta 1986 zuwa 1989 Inda ya samu shaidar kammala makarantar babbar sakadire.

      MATAKAN KARATU NA GABA DA SAKANDIRE.

Bayan karkare matakin karatun sakandire cikan nasara Dakta ya shila izuwa makarantar Jami'a ta UNIMAID dake garin Maiduguri a jihar Borno a shekara ta 1986 zuwa 1998 inda ya samu shidar kammalawa a bangaren kula da lafiyar dabbobi daga nan sai kuma sake samu nasarar shiga makarantar Gem professional computer Calabar inda ya samu shaidar karatu a bangaren na'ura mai kwakwalwa bayan nan sai ya zarce zuwa Makarantar Fasaha na gwamnatin tarayya dake garin Damaturu inda ya samu shaidar kammala karatun Difiloma a bangaren shari'a, Daga nan sai kuma kwalejin veterinary surgeon na Nijeriya inda ya samu damar zama veterinary fellow/consult a 2020.


            AIYUKA

Ya fara aiki a mataki na farko a lokacin da yake aikin yiwa kasa hifima NYSC a wani asabitin dabbobi dake garin Calabar bayan ya kammala aikin wiya kasa hidima ne ya samu nasarar kama aiki a gwamnatin jihar Yobe a asibitin dabbobi dake garin Nguru shekara ta 2000.

Bayan wannan lokaci ne kuma ya samu canjin gurin aiki a shekara ta 2003 zuwa asibitin dabbobi dake gari Gashuwa a matsayin Veterinary officer, Shekara guda da faruwar haka na sake samu karin girma da canjin gurin aiki a shekara ta 2004 izuwa matakin Zonal veterinary officer a garin Geidam. Daga nan sai kuma wata canjin zuwa garin Potiskum a shekara ta 2005 a matakin Farm manager , bayan wasu takaitaccen lokaci sai kuma wani karin girman zuwa matsayin Bird flu surveillance agent a hedikwatar gwanatin jihar yobe a shekara ta 2006 bayan kwashe shekara guda sai kuma samun karin girma zuwa matsayin head of Animal health a shekara ta 2007 tun daga waccan lokaci sai kuma wannan shekara ta 2020 na sake samu karin girma zuwa Program Manager.

      MUKAMAN SARAUTA.

Ya samu nadi na farko a matsayin Galadiman Dozi a shekara ta dubu biyu da goma sha hudu 2014, Sai kuma a shekara ta dubu biyu a ashiri 2020 ya sake samu wata sabuwar nadin daga Masarautar Gudi dake karamar hukumar Fika a matsayin Zarma kuran Gudi.

             KALUBALE

Rasuwar yaya a gurinshi bayan ya rasa iyaye naga cikin manyan kalubale da ya fuskanta a cikin rayuwar shi, sai kuma matsala irin ta wakiltar jama'a wadda abu ne mai wahala ka iya yiwa kowa yadda yake so sai dai iya gwargwadon iyawarka kuma tsakanin ka da Mahaliccinka wannan sune kubale dana fuskanta a takaice.

           NASARORI

Hakika na cimma nasarori masu tarin yawa a ciki rayuwata kuma ina alfari da hakan.


  FITATTUN AL'AMURA

A-kungiyoyi

1- Yayi sakatare kuma shugaban Nigeria veterinary medical association na jihar yobe daga 2006 zuwa 2013

2- yayi sakataren poultry association of Nigeria daga 2006 zuwa 2011

3- shine shugaban join health workers na jihar yobe

B- gwamnatin jihar yobe

1-memba a review of medical worker's

2-memba a agricultural revitalization implementation comitee

3-memba a faculty of agriculture establishment a jami'ar jihar yobe

4-shine sakataren committee for the collection of livestock Tax
                  FATA

Allah ya bani ikon yiwa al'umma fiye da abunda nake musu a baya, sannan na baya suyi koyi cewa maraici bashi ne karshen rayuwa ba. Muhammad Musa Tika (talk) 07:12, 24 ga Afirilu, 2022 (UTC)Reply

Muhammad Musa Tika Muhammad Musa Tika (talk) 06:34, 26 ga Afirilu, 2022 (UTC)Reply