Suranci
harshe
(an turo daga Tapshinanci)
Suranci (Sur-Myet, kuSur, Tapshin) harshe ne na dangin harsunan a jahar Filato na jihohin Bauchi da Filato dake Nijeriya. Akwai harsuna biyu da ke da kusanci da yaren Súr da Myet.
Suranci | |
---|---|
Lamban rijistar harshe | |
ISO 639-3 |
tdl |
Glottolog |
surr1238 [1] |
Akwai akalla masu amfani da harshen Sur–Myet sama da mutum 16,000.[2] Masu amfani da harshen Sur suna gewaye da 'yan yaren Ngas, wadanda ke kiran mutanen Sur da Dishili.[3] Duk da haka, harshen Sur ya kasance harshe ne mai muhimmanci kuma har yanzu ana koya wa kananan yara, sannan kuma ba ya cikin harsunan da ke cikin haɗarin bacewa.[4]
Wuraren da mutanen Sur suke
gyara sasheAna amfani da harshen Sur a wadannan kauyuka.
- Kancak
- Targal
- Kantem
- Shishir
- Gyasham Sakiya
- Kalep
- Mashekarah
- Bussa
- Kocten Angwan Gyad
- Shikanyan
- Bakin Kogi Pwai
- Bada Koshi
- Nasarawa Pwai
- B. Kogi Tapshin (ana kuma kiran kauyen Tapshin village da suna Ngotuk)
Sannan kuma ana amfani da harshen Myet a wadannan kauyuka
- Myet
- Gat Myet
- Dasham
- Dasham Yelwa
- Pukdi
- Yimi
- Nkandim
Duba kuma
gyara sasheManazarta
gyara sashe- ↑ Hammarström, Harald; Forkel, Robert; Haspelmath, Martin, eds. (2017). "Suranci". Glottolog 3.0. Jena, Germany: Max Planck Institute for the Science of Human History.
- ↑ Decker, Ken, Yakubu Danladi, Julius Dabet, Benard Abraham, Innocent Jonah. 2021. A Sociolinguistic Profile of the Kusur-Myet (Sur) [tdl] Language of Plateau and Bauchi States, Nigeria. Journal of Language Survey Reports, 2021-023. SIL International.
- ↑ Blench, Roger M. 1998. Recent fieldwork in Nigeria: Report on Horom and Tapshin. Ogmios, 9:10-11.
- ↑ Blench, Roger. 2004. Tarok and related languages of east-central Nigeria.