Annabi Isah
Annabi Isa (A.S) na daya daga cikin Annabawa a Musulunci.[1] Wanda Allah ya aiko.
Annabi Isah | |||
---|---|---|---|
← John the Baptist in Islam (en) - Muhammad in Islam (en) → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Herodian Kingdom of Judea (en) , | ||
Mutuwa | no value, no value | ||
Ƴan uwa | |||
Mahaifiya | Maryam a Musulunci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Mai da'awa da missionary (en) | ||
Imani | |||
Addini | Musulunci |
Nasabar Annabi Isah (A.S)
gyara sasheSunan mahaifiyarsa Maryam Imrana. Sunan Mahaifiyarta Hannatu, mahaifinta yana cikin manyan mutane a cikin jama'ar Banu-Isra'ila har ma shi ne yake limanci a Masallacin Qudus.
Yayinda matar Imrana ta sami cikinsa ta rika fatan abin da za ta haifa ya zama namiji har ma ta yi bakance idan ta haifi namiji zai zama hadimin masallaci, amma da ta tashi haihuwa sai Allah ya ba ta 'ya mace. Hannatu babar Maryam ta damu qwarai saboda bakancen da ta yi, amma duk da haka sai ta yi wa Allah godiya kuma ta ambace ta da suna Maryam, Ma'anarsa shi ne, WADDA BA TA DA AIBI.
Iyayen Maryam sun rasu tana qarama saboda haka sai Annabi Zakariyya ya dauke ta ya cigaba da renonta, har ma ya gina mata ɗaki na musamman a cikin Masallaci. Babu wanda yake shiga dakin sai shi. Nana Maryam tun tasowarta ba ta da wani aiki sai ibada dare da rana. Duk sanda Annabi Zakariyya ya kawo mata ziyara sai ya tarar da abinci da kayan marmari a wajenta, idan ya tambayeta wa ya kawo mata wannan sai ta ce: Daga Allah ne, domin Allah yana arzuta wanda ya so, ba tare da hisabi ba.
Annabi Isah (A.S)
gyara sasheYayin da Nana Maryam ta kai munzalin girma sai al'ada ta zo mata, saboda haka, sai ta fita bayan gari wajen wata qorama don ta yi tsarki, sai Mala'ika Jibril ya zo mata a siffar wani saurayi daga Banu Isra'ila mai suna Taqiyyu, shi wannan mutum ya yi qaurin suna da ɓarna a wannan lokaci Allah Madaukakin Sarki ya ce, "Sai muka aika mata da ruhu (shi ne Mala'ika Jibrilu) ya je mata a surar saurayi, sai ta ce "Ni ina neman tsari da Ubangijin Rahama daga gareka idan kai ne Taqiyyu. "Sai Mala'ika Jibril ya ce, mata "Ni Manzon Ubangijinki ne, Allah ne ya aiko ni. Domin in ba ki kyautar ɗa mai qwazo.[2]
"Sai ta ce da shi: Ta ya ya zan sami ɗa, bayan wani mutum bai shafe ni ba, kuma ni ban taɓa yin alfasha ba? Sai ya ce: Haka al'amarin yake, haka Allah Ya hukunta, kuma wannan abu ne mai sauqi a wajen Allah. Allah ya ce: "Za mu sanya shi ya zama izina a wajen mutane, kuma Rahama daga garemu, wannan lamari ne zartacce." (Surar Maryam, Aya ta 17) Mala'ika Jibrilu yana gama wannan bayanin sai ya kama gefen rigarta ya yi busa a ciki, nan take sai Allah ya halicci Annabi Isah a cikin cikinta. Malam wahabu ya ce: Tsakanin ɗaukar cikin Annabi Isah da haifarsa sa'a guda ne kawai, saboda faɗin Allah Ta'ala ya ce, "Sai ta ɗauki cikinsa, sai ta tafi da shi wuri mai nisa, sai naquda ta zo mata a wajen kututturen dabino, sai ta ce: Ya kaicona dama na mutu kafin faruwar wanan na zama mantacciya abar mantawa."
Sai Allah ya ce; Sai muka kirata ta qarqashinta muka ce: Kada ki yi baqin ciki, Allah ya gudano da qoramar ruwa a kusa da ke, ki girgiza kututturen dabinon nan zai zubo miki da lubiya nunanniya, ki ci, ki sha, ki kwantar da hankalinki. An ce wannan dabinon da ta girgiza shekararsa saba'in bai yi 'ya'ya ba, amma ana haihuwar Annabi Isah a kusa da shi, nan take sai ya yi ganyen, ya fitar da 'ya'ya saboda mu'ujizar Annabi Isah (A.S.)
Ruwaya
- An ruwaito cewa; Yayinda Maryam ta je wajen mutanenta tana ɗauke da Annabi Isah (A.S.) sai suka ce; Ya ke Maryam lallai kin zo da babban lamari, ya 'yar'uwar Haruna mahaifinki ba mutumin banza ba ne, mahaifiyarki ma ba mutuniyar banza ba ce. Yayinda ta ji wannan zargi daga mutanenta sai ta yi musu nuni da Annabi Isah tana nufin su tambaye shi. Sai suka ce: Ta ya ya za mu yi magana da jariri a cikin zanin goyo?
Sai Allah ya buɗi bakin Annabi Isah ya ce da su:
"Ni bawan Allah ne ya bani littafi yasan yani Manzo yayi albarka a gareni duk inda nake yayimin wasiyya da sallah da Zakka matukar ina raye, sannan da yin biyayya ga Mahaifiyata. Bai san yani shakiyyi mai girman kai ba, farkon Kalmar da Annabi Isah ya fara magana da ita itace, ni bawan Allah ne domin yanke hanzari ga wadanda za suce shi dan Allah ne.
- Anruwaito cewea yayin da Annabi Isah ya girma sai yarika yawo aba yan kasa, baya zama da waje daya, saboda haka ma bai taba mallakar dakin kwana ba. Bare gida ko mata, ko abun hawa tufafinsa kuma jubbace ta sufi. Baya cin abinci sai daga kasabin Mahaifiyarsa ta kasance tana saka tufafi tasiyar suci abinci. a irin wayace-wayacen da yake yi ya je wani gari da ake cewa Nasira a qasar Sham, shida mahaifiyarsa suka zauna a can.
Saboda haka ne ake dan ganta mutanensa da sunan wannan garin ake ce musu NASARA.
Mu'ujizar Raya Uzairu (A.S.)
gyara sasheMalam Wahabu ya ce; Yayin da lamarin Annabi Isah ya shahara da cewa yana raya matacce ya warkar da makaho, da izinin Allah sai Yahudawa suka taru suka je wajensa suka ce, mu ba zamu yi imani da kai ba har sai ka raya mana Uzairu. Sai ya ce da su: A ina kabarinsa yake? Sai suka kai shi inda kabarin yake, sai ya yi sallah raka'a biyu ya roqi Allah ya raya masa Uzairu. Saiu aka ga kabarin yana buxewa a hankali a hankali, sai ga Uzairu ya bayyana. Gashin kansa da gemunsa sun yi fari, sai ya cewa Annabi Isah, :Ya xan Maryamu wannan shi ne abinda zaka yi min? Sai Annabi Isah ya ce: Mutanenka ne suka ce ba za su bada gaskiya da ni ba sai na tashe ka. To daga nan sai Uzairu ya tashi zaune, ya ce: Ya ku jama'ar Banu Isra'ila ku yi imandi da Manzancin Annabi Isah, ku bi addininsa, shi a kan gaskiya yake,d aga Ubangijinsa, sai Yahudawa suka ce da shi: To ai mu kafin ka mutu mun san saurayi ne kai matashi mai baqin gashi ya ya muka ganka yanzu kanka ya yi fari fat? Sai ya ce: Yayin da Annabi Isah ya ce min tashi da izinin Allah na zaci tashin kiyama ce, saboda haka ya sa nan take kaina da gemuna suka yi fari, yayin da Annabi Isah ya raya Uzairu da mu'ujiza, sai mutane da yawa daga cikinsu suka bada gaskiya da shi, sannan daga bisani sai ya roqi Allah ya mayar da Uzairu matacce kamar yadda yake.
Ambaton saukar ma'ida
- An ruwaito daga Salmanul Farisi (R.A.) ya ce: hawariyawa sun faxa ga Annabi Isah suka ce shin Ubangijinka zai iya suako mana da Ma'ida daga sama? Sai ya'amsa musu ya ce, ku dai ku ji tsoron Allah in kun kasance muminai, sai suka ce lallai muna da buqatar haka, sai Annabi Isah ya fita ya shiga sahara ya yi ta kuka yana qanqan da kai ga Allah yana cewa: "Ya Ubangiji ka saukar mana da Ma'ida daga sama domin ta zama idi ga na farkonmu da na qarshenmu, ta kasance aya daga gareka, ka arzurtamu kai ne fiyayen mai arzutawa."
Sai Allah ya yi wahayi gare shi ya ce: "Ni zan saukar da ita gareku, amma wanda duk ya kafirta a cikinku bayan wannan haqiqa zan masa azaba irin wadda ban tava yiwa wani irinta ba, a cikin talikai."
- Imamutturmuzi ya ce: Sai Allah ya saukar musu da teburin abinci daga sama a tsakanin giragizai guda biyu, yayin da Annabi Isah ya ganta sai ya ce: Ya Ubangiji ka sanya ta zama Rahama, kada ta zama azaba.
Ba ta gushe ba tana saukowa a hankali a hankali har sai da teburin abincin nan ya sauko qasa mutane na kallo an lulluve shi da mayafi, sai Annabi Isah ya fadi ya yi sujjada ga Allah ya yi godiya. Hawariyawa suma suka yi sujjada tare da shi, sannans uka ce Annabi Isah ya tashi ya bude su ga abinda yake ciki. da aka bude sai ga soyayyen kifi da zaitun da dabino da gurasa, da wani nau'in kayan marmari. Sannan sai Annabi Isah ya cewa kifin nan tashi da izinin Allah, sai Allah ya raya kifin ya riqa juyawa yana kallon jama'ar Banu Isra'ila, sannan sai ya cewa kifin ya koma yadda yake da izinin Allah. sai Hawariyawa suka cewa Annabi Isah shi ya kamata ya fara cin abincin nan. Sai ya ce: A'a wanda ya nemi a kawo shi zai ci. sai duk suka qi ci, suna tsoron kada ta zama fitina, sai ya sa aka kirawo talakawa da miskinai da guragu da makafi, ya ce su ci. A cikinsu har da marasa lafiya da masu cutar albasar da sauransu duk suka haxu suka ci abincin. Suna gama ci marasa lafiyar nan sai duk suka warke, nan take. Yayin da mutanen gari suka ji labari sai suma suka zo suka ci, har suka riqa turereniya, da Annabi Isah ya ga haka sai ya sa aka kasa mutane kashi biyu, rana daya ta talakawa, rana daya kuma ta mawadata.
Sai Ma'idar ta zama tana sauka sau daya bayan kwanaki biyu. Sannan kuma wannan tebur idan ya sauka duk yawan mutanen da suke wajen kowa zia ci ya qoshi, ya bari sannan ya tashi ya koma sama kamar yadda ya sauko. An ce haka Ma'idar nan ta riqa sauka har tsawon kwana arba'in. Sannan sai wata jama'a daga Bani Isra'ila suka aibata Ma'idar suka ce ba Allah ne yake saukar da ita ba, da suka faxi haka, sai Allah ya mayar da wasunsu aladu, wasu kuma birori. An ce adadin waxanda suka haxu da wannan matsala sun kai mutum talatin, suka zuana a cikin wannan hali tsawon kwanaki bakwai sannan sai qasa ta haxiye su.
Yuqurin kashe Annabi Isah (A.S.)
gyara sasheKa'abur Akabari ya ce; Yayin da addinin Annabi isah ya yaxu ya cika ko'ina, mutane suka yi ta shiga addinin daga ko'ina, sai addinin Yahudanci ya yi rauni, Allah ya saukarwa Annabi Isah Littafin Linjila, ya zama yana raya matattu da ikon Allah, yayin da wani sarki mai suna HArdusa ya ga haka sia ya yi nufin zai kashe Annabi Isah (A.S.) ya sami goyon bayan wasu daga manyan malaman Yahudawa. Sai suka shirya suka ki masa hari a lokacin yana tare da mahaifiyarsa suka wakilta wani daga cikinsu don ya shiga xakin ya kashe shi. Kafin ya shiga sai Allah ya xauke Annabi zuwa sama, ya shiga yanan ta dube-dube bai gan shi ba, sauran waxanda suke waje da suka ga ya daxe bai fito ba sai suka bi shi suna shiga sai suka ga xan uwansu, Allah ya sa masa kamannin Annabi Isah komai da komai, sai suka kama shi suka xaure suka sa masa hular gashi, suka kewaye gari da shi, sannans uka kafa azarori guda biyu suka gicciye shi a kanta, suka kashe xan uwansu, suna zaton Annabi Isah suka kashe.
Allah Madaukakin Sarki ya ce; "Ba su kashe shi ba, ba su gicciye shi ba, sai dai cewa Allah ya xuakaka shi ya zuwa gare shi. An ruwaito cewa: A lokacin da suka kashe xan uwansu ya kasnace ranar Juma'a ne da misalin qarfe uku na rana, sai duniyad ta yi duhu, tsawon kwanaki uku, a kai girgizar qasa a wanan rana.
Malam Sa'alabi ya ruwaito cewa: Lokacin da aka xauke Annabi Isah zuwa sama shekarunsa talatin da biyar a duniya. Sai Allah Ta'ala ya sara masa xabi'a irin ta Mala'iku ya zama baya buqatar ci da sha, kuma har yau yana nan a raya kamar yadda Hadisai ingantattu suka tabbatar.
Malam Sa'alabi ya qara da cewa: nana Maryam Allah ya qara mata yarda ta yi wafati bayan xauke Annabi Isah da shekara shida. An ce ta rayu tsawon shekara sittin. Kabarinta a yanzu haka yana masallacin qudus ana ziyararsa.
Saukowar Annabi isah (A.S) zuwa Kasa
gyara sasheMalam Uwaisu Assakafi ya ruwaito cewa: Na ji Manzon Allah (S.A.W.) yana cewa: "Annabi Isah dan Maryam zia sauko daf da tashin alqiyama, zai sauka a kan wata hasumiya fara da take a gabashin masallacin Dimashka.
Annabi Isah mutum ne mai madaidaicin tsawo mai baqin gashi, mai farin launi, idan ya sauka zai shiga masallaci ya zuana a kanmubari sai mutane su ji labarin saukarsa, sai su yi ta shiga masallacin, ta ko'ina Musulmai da Kirista da Yahudawa, aka cika masallacin har ta kaid wasu akan wasu, saboda ci kowa.
Sannan sai mai kiran sallah daga Musulmi ya kira sallah, sai Annabi isah ya shige gaba ya yi limanci, a sannan Imamu Mahadi, ya bayyana kuma yana cikin masallacin sai ya bi sallar ita ce sallar Asuba.
Bayyanar Dujal
gyara sasheAn ruwaito cewa a lokacin da Dujal zai bayyana zai fito daga garin Asfihan tsawonsa zira'i goma, kuma ido xaya ne da shi, an rubuta (KAFIR) a fuskarsa. A qasan wannan kuma an rubuta: DUK WNADA YA BI SHI YA TAVE, WANDA YA QI SHI YA YI ARZIQI, ya na nunawa mutane yana da wuta da aljanna, amma a haqiqa wutarsa aljannace, aljannarsa kuma wuta ce. Zai kewaye duniya yana kashe mutane yana cewa shi ne Ubangiji. Yana tafe da dubunnan xaruruwan sojoji, zia biyo ta Asfihan ya zo Dimashqa. A cikin kwana arba'in, ya yi ta kashe mutane yana ribace su, to a sannan Mahadi zai bayyana sai mutane su taru a qarqashinsa ya xaura xamarar yaqar Dujal.
Ana cikin haka sai Annabi Isah ya sauka sai su haxu da Mahadi, a wannan maslalaci su yi sallah tare, kamar yadda bayani ya gabata. Sai Dujal ya fito da rundunarsa don ya yaqe su, yanayin arba da Annabi Isah sai ya narke kamar yadda darma take narkewa a kan wuta, sai Annabi Isah ya kashe shi da takobinsa.
An ruwaito cewa bayan kashe Dujal Annabi Isah zai shimfixa mulki na adalci a bayan qasa, ba zai bar wani Bayahude ko Banasare akan addininsa ba, sai Musulunci kawai, zai yi hukunci da adalci a tsakanin mutane, gabas da yamma, kudu da arewa. Asannan Allah zai umarci qasa da ta fito da alheranta ga mutane, kamar yadda ta kasance tun da farko, har ta kai ga mutane da yawa za su haxu a kan curi xaya na inibi su ci har su qoshi amma ba zai qare ba, yaro ya xauko maciji yana wasa da shi, amma ba zai cuce shi ba, akuya ta haxu da aki amman ba zai kulata ba. Mutane kowa zai rayu a cikin yalwa da wadata har ta kai za a ba mutum kyautar kuxi ya ce, baya buqata. Mutum zai ga kabari sai ya ce: Ina ma dai wannan yana raye ya ga irin adalcin da yake gudana a bayan qasa. Za a kasance a wannan hali tsawon shekara arba'in. Sannan sai Annabi Isah ya auri wata mata daga mutanen Askalan ta haifa masa 'ya maza guda biyu, sai ya tafi Makka ya yi aikin Hajji, ya je Madina ya ziyarci Annabi (S.A.W) Sai ya yi rashin lafiya, sai Allah ya karvi ransa, anan Madina, sai a binne shi a cikin Raudah kusa da Annabi (S.A.W.).
Fa`ida Idan Dujal ya bayyana zai shiga ko'ina amma ban da Makka da Madina, duk sadda ya zo zai shiga sai ya ga Mala'iku sun tsaitsaya suna gadin garin sai ya koma.
Tsari daga Dujal Sannan ya inganta a Hadisi Annabi (S.A.W) ya ce: Duk wanda ya haddace ayoyi goma na farkon Suratul Kahfi, Allah zia kiyaye shi daga fitinar Dujal.