Sylvester Anyanwu

Dan siyasar Najeriya

Sylvester Udubuisi Anyanwu (an haife shi ranar 26 ga watan Mayun shekarar 1951) an zaɓe shi a matsayin Sanata mai wakiltar Imo ta Arewa (Okigwe) na jihar Imo, Najeriya, ya karɓi mulki a ranar 29 ga watan Mayun shekara ta 2007. Ɗan jam'iyyar PDP ne.[1]

Sylvester Anyanwu
mutum
Bayanai
Bangare na Nigerian senators of the 6th National Assembly (en) Fassara
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Suna Sylvester (mul) Fassara
Shekarun haihuwa 26 Mayu 1951
Wurin haihuwa Jahar Imo
Sana'a ɗan siyasa
Muƙamin da ya riƙe mamba a majalisar dattijai ta Najeriya
Ɗan bangaren siyasa Peoples Democratic Party

Anyanwu ya samu digirin farko a fannin lissafi, tattalin arziƙi da kuma digiri na biyu a fannin harkokin kasuwanci (finance).[1] Ya yi aiki a matsayin ma'aikacin banki a ƙasar waje na tsawon shekaru kafin ya dawo Najeriya. Ya taɓa zama mamban matasa a hukumar kwastam ta Najeriya, sannan ya shiga aikin soja.[2] Daga nan ya zama kwamishinan kasuwanci da masana’antu na jihar Imo kuma shugaban kamfanin siminti na Nkalagu.[1]

Bayan ya hau kujerar sa a Majalisar Dattawa an naɗa shi kwamitocin Jihohi & Ƙananan Hukumomi, Kimiyya da Fasaha, Asusun Gwamnati, Neja Delta da Sadarwa (Chairman).[1] A cikin tantancewar tsakiyar wa'adi na Sanatoci a cikin watan Mayun shekarar 2009, ThisDay ya ba shi maki "matsakaici", lura da cewa ya ɗauki nauyin ƙudirin kafa Cibiyar Kula da Baitulmali kuma ya kasance mai aiki a Kwamitin Sadarwa.[3] Da yake magana kan jihar Imo, da ma Najeriya baki ɗaya, a wata hira da aka yi da shi a cikin watan Mayun shekarar 2010, ya ce a zaɓe mai zuwa na shekarar 2011 duk wani ɗan majalisar dattawa, gwamna ko shugaban ƙaramar hukuma da ke neman sake tsayawa takara dole ne ya nuna abubuwan da ya cimma. Ya bayyana samar da wutar lantarki da inganta tsaro a matsayin batutuwa na farko.[4]

Manazarta

gyara sashe