Suya

Suya kalma ce da ake amfani da ita don bayyana ɗan abin ci na naman da aka yanka a Afirka, musamman a Najeriya da Kamaru. Yawanci ya samo asali ne daga Hausawa, ɗaya daga cikin manyan kabilu a Yammacin Afirka.

Suya ko Tsire nama ne mai yaji wanda sanannen abinci ne a yammacin Afirka.[1] Ana kuma ci a Sudan, ana kiranta da "Agashe".[2] Ana yin Suya ne da naman sa, rago, ko kaza. Hakanan ana amfani da kayan ciki kamar koda, hanta da zuciya.[3] Yankakken naman ana daka shi da kayan kamshi daban-daban wadanda suka hada da gyadar Qamshi, gishiri, magi, mai da sauran kayan kamshi. sannan a barbecue, ana hadawa Suya da karin taimako na busasshen barkono da aka hada da kayan kamshi da yankakken albasa. Ana amfani da hanyoyin shirya naman halal ne, musamman a yankunan arewacin Najeriya,[3] inda aka san rashin dacewa da haramcin abincin musulmi a shirin Suya na haddasa tarzoma.[4] Busashen Suya ana kiransa Kilishi.[3] Ana iya ci da Garri ko Ogi.

Suya
meat dish (en) Fassara
Kayan haɗi nama, cayenne pepper (en) Fassara, Rago, Kaza, Skewered Goose Liver (en) Fassara da tripe (en) Fassara
suyan tsire
suyan tsire
Suya da yaji
Suya
Madadin sunaye Agashe (Sudan) Tsire (Arewacin Nigeria)
Yanki ko jiha Najeriya
Babban sinadaran Nama, kaza, jatan lande
Bambance-bambance Kilishi
Mai sayar da Suya a Abuja.
Suya kaza da jollof rice da plantain

Babu daidaitaccen girke-girke na samar da hadadden cakuda kayan yaji da abubuwan da suka hada da suya marinade (wanda ake kira Yaji) da kayan yaji da aka yi amfani da su. Sinadaran na iya bambanta dangane da abubuwan da mutum yafi son amfani dasu da na yanki.[3]

Duk da cewa Suya ta samo asali ne daga sassan Arewacin Najeriya, amma ta shiga cikin al’ummar Najeriya, tana da araha ga kowa da kowa kuma a ko’ina. An kira shi wani abu mai haɗa kai a Najeriya.[5] Suya ya zama abincin Najeriya da yankuna daban-daban da ke ikirarin fifikon girke-girke da hanyoyin shirya su, amma irin gasasshen nama ya zama ruwan dare a yawancin kasashen yammacin Afirka.[3]

Manazarta

gyara sashe
  1. EKE, IRABOR ,OKOYE; et al. "THE MICROBIAL STATUS OF COMMERCIAL 'SUYA' MEAT PRODUCTS IN EKPOMA, EDO, NIGERIA" (PDF). International Journal of Community Research. Archived from the original (PDF) on 24 September 2021. Retrieved 5 April 2014.CS1 maint: multiple names: authors list (link)
  2. El-Sheikh, Amr (3 December 2018). "Agashe: Sudan's Homage to its African Roots". 500 Words Magazine. Retrieved 22 Mar 2020.
  3. 3.0 3.1 3.2 3.3 3.4 Agence France-Presse (22 May 2012). "Nigerian roadside barbecue shacks thrive in the midst of Islamist insurgency". The Raw Story. Archived from the original on 7 April 2014. Retrieved 5 April 2014.
  4. Jacobs, Alan (18 January 2008). "Suya Wars". First Things. Archived from the original on 4 April 2014. Retrieved 5 April 2014.
  5. GAMBRELL, Jon (24 November 2012). "Suya, the thin-sliced spiced meat, unites Nigeria". Ann Arbor News. Retrieved 2 April 2014.6. Fatinbaba1 (8/7/2024) Suya, tsire unites in Nigeria.