Suranci (Sur-Myet, kuSur, Tapshin) harshe ne na dangin harsunan a jahar Filato na jihohin Bauchi da Filato dake Nijeriya. Akwai harsuna biyu da ke da kusanci da yaren Súr da Myet.

Suranci
Lamban rijistar harshe
ISO 639-3 tdl
Glottolog surr1238[1]

Akwai akalla masu amfani da harshen Sur–Myet sama da mutum 16,000.[2] Masu amfani da harshen Sur suna gewaye da 'yan yaren Ngas, wadanda ke kiran mutanen Sur da Dishili.[3] Duk da haka, harshen Sur ya kasance harshe ne mai muhimmanci kuma har yanzu ana koya wa kananan yara, sannan kuma ba ya cikin harsunan da ke cikin hadarin bacewa.[4]

Wuraren da mutanen Sur suke gyara sashe

Ana amfani da harshen Sur a wadannan kauyuka.

  • Kancak
  • Targal
  • Kantem
  • Shishir
  • Gyasham Sakiya
  • Kalep
  • Mashekarah
  • Bussa
  • Kocten Angwan Gyad
  • Shikanyan
  • Bakin Kogi Pwai
  • Bada Koshi
  • Nasarawa Pwai
  • B. Kogi Tapshin (ana kuma kiran kauyen Tapshin village da suna Ngotuk)

Sannan kuma ana amfani da harshen Myet a wadannan kauyuka

  • Myet
  • Gat Myet
  • Dasham
  • Dasham Yelwa
  • Pukdi
  • Yimi
  • Nkandim

Duba kuma gyara sashe

Manazarta gyara sashe

  1. Hammarström, Harald; Forkel, Robert; Haspelmath, Martin, eds. (2017). "Suranci". Glottolog 3.0. Jena, Germany: Max Planck Institute for the Science of Human History.
  2. Decker, Ken, Yakubu Danladi, Julius Dabet, Benard Abraham, Innocent Jonah. 2021. A Sociolinguistic Profile of the Kusur-Myet (Sur) [tdl] Language of Plateau and Bauchi States, Nigeria. Journal of Language Survey Reports, 2021-023. SIL International.
  3. Blench, Roger M. 1998. Recent fieldwork in Nigeria: Report on Horom and Tapshin. Ogmios, 9:10-11.
  4. Blench, Roger. 2004. Tarok and related languages of east-central Nigeria.