Surajudeen Ishola Adekunbi ɗan kasuwar Najeriya ne kuma ɗan majalisar dokokin jihar Ogun, inda shine shugabanta mai ci.[1]

Suraj Adekunbi
Rayuwa
Haihuwa 8 ga Maris, 1975 (49 shekaru)
Karatu
Makaranta Babban Makarantar Sakandare, Aiyetoro
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Rayuwar farko

gyara sashe

An haife shi a Ayetoro, dake jihar Ogun a kudu maso yammacin Najeriya, Adekunbi yana ɗaya daga cikin ƴaƴa goma sha biyar na Rahmon da Elizabeth Adekunbi.[2]

 
Suraj Adekunbi

Ya halarci makarantar firamare ta St. Paul African Church, Ayetoro, kafin ya wuce zuwa makarantar Sakandare ta Aiyetoro, inda ya samu takardar shedar makaranta a shekara ta alif dari tara da casa'in da uku 1993. Ya samu Diploma ta ƙasa a fannin Injiniya daga Federal Polytechnic, Ilaro a shekarar ta alif dari tara da casa'in da shida 1996, sannan ya sami Diploma ta ƙasa a Polytechnic, Ibadan. Daga nan ya sami takardar shaidar kammala karatun digiri a jami'ar fasaha ta tarayya dake Akure, da kuma digiri na biyu a fannin raya ayyuka da aiwatarwa a shekarar 2011 a jami'ar Ibadan.[3]

Sana'a Da Siyasa

gyara sashe

Adekunbi ya fara aikin sa ne da aiki a matsayin mataimaki na aiki a Kamfanin Bunƙasa Man Fetur (NPDC) da ke Jihar Edo a lokacin da yake hidimar matasa masu yi wa ƙasa hidima a shekarar 2000. Bayan ya yi hidimar Matasa, ya koyarwa a Government Technical College, Idi-Aba, Abeokuta. Daga nan ya shiga ma’aikatan gwamnatin jihar Ogun yana aiki a ofishin sufuri daga shekarar 2004 zuwa 2006, kafin daga bisani ya ajiye aiki ya koma kamfanin mahaifinsa, Al-Rahman Oil & Gas Limited.[3][2]

A shekarar 2007, ya tsaya takarar ɗan majalisar dokokin jihar Ogun a Egbado North (yanzu Yewa North) amma ya sha kaye.[ana buƙatar hujja]A cikin shekarar 2011 ya sake tsayawa jam'iyyar Action Congress of Nigeria (ACN) kuma ya yi nasara. An kuma zaɓe shi a matsayin shugaban majalisa.[4] kuma aka sake zaɓen shi a matsayin Kakakin Majalisa a 2015.[5][6][3]

Manazarta

gyara sashe
  1. http://thenationonlineng.net/adekunbi-returned-as-ogun-speaker/
  2. 2.0 2.1 "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2017-09-06. Retrieved 2023-03-16.
  3. 3.0 3.1 3.2 "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2023-03-16. Retrieved 2023-03-16.
  4. https://www.vanguardngr.com/2011/06/ogun-edo-get-new-speakers/
  5. https://thenewsnigeria.com.ng/2015/06/08/adekunbi-returns-as-ogun-assembly-speaker/
  6. https://www.legit.ng/456409-adekunbi-re-elected-ogun-speaker.html[permanent dead link]