Sunday Omobolanle
Sunday Omobolanle aka Papi Luwe, MON (an haife shi a ranar 1 ga watan Oktoban 1954) ɗan wasan barkwanci ne na Najeriya, marubucin wasan kwaikwayo, kuma mai bada umarni da shirya fina-finai.[1][2]
Sunday Omobolanle | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Jahar Oyo, 10 ga Janairu, 1954 (70 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Yarbanci |
Karatu | |
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | jarumi |
Rayuwar farko da aiki
gyara sasheAn haife shi a ranar 1 ga Oktoba, 1954 a Ilora, wani gari a jihar Oyo a kudu maso yammacin Najeriya.[3] Shi ne mahaifin Sunkanmi Omobolanle, jarumin fim na Najeriya kuma mai bada umurni. [4] Sunday Omobolanle ya rubuta, ya ba da umarni, ya shirya kuma ya fito a cikin fina-finan Najeriya da dama kamar Adun Ewuro, wani fim na Najeriya na 2011 wanda ya fito da Adebayo Salami . A bisa gudunmawar da ya bayar a masana’antar shirya fina-finai ta Najeriya, ya samu lambar yabo ta kasa, MON wanda tsohon shugaban Tarayyar Najeriya Olusegun Obasanjo ya ba shi.[5]
Fina-finai
gyara sashe- Adun Ewuro (2011)
- Konkobilo
- Oba Alatise
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2015-02-21. Retrieved 2021-12-23.
- ↑ Latestnigeriannews. "RMD, Aluwe, 32 others in Glo new campaign". Latest Nigerian News (in English). Retrieved 2021-08-23.CS1 maint: unrecognized language (link)
- ↑ "ALUWE SUNDAY OMOBOLANLE". Modern Ghana (in Turanci). Retrieved 2021-08-23.
- ↑ "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2016-10-11. Retrieved 2021-12-23.
- ↑ "Nollywood/ Nigeria No.1 movies/ films resources online". www.nigeriafilms.com. Retrieved 2021-08-23.