Stefania Filo Speziale (1905 -1988) yar asalin ƙasar Italiya ce, mace ta farko da ta kammala digirinta daga cikin shirin gine-gine a Naples, Italiya.

Stefania Filo Speziale

Tarihin rayuwa da Karatu gyara sashe

An haife ta a Naples kuma ta sauke karatu daga Regio istituto superiore di architettura a Naples a shekara 1932. Filo Speziale ta yi aiki a matsayin mataimakiya ga farfesa Marcello Canino a Faculty of Architecture a Jami'ar Naples. Ta zama cikakkiyar farfesa a 1970.

A cikin shekara 1930s, ta kasance mai zane-zane a Mostra d'Oltremare, tana zana rumfunan da yawa. Bayan haka, ta yi aiki a kan gidaje masu zaman kansu da gidajen jama'a a Naples. Ta kasance memba na National Institute of Urban Design a shekara1945. Ta tsara Cinema na Metropolitan a Naples cikin shekara 1948. Ta yi aiki tare da masu zane-zane biyu Carlo Chiurazzi da Giorgio di Simone tun daga 1954; sun fara a matsayin mataimaka amma daga baya suka raba ofis da ita. Mafi kyawun aikin su ya haɗa da Palazzo Della Morte da Cattolica Assicurazioni skyscraper.

Mutuwa gyara sashe

Ta mutu a Naples a shekara 1988.

Manazarta gyara sashe