Sokoto (kogi)
Kogin Sokoto (wanda aka fi sani da Gulbi 'n Kebbi,) kogi ne a arewa maso yammacin Najeriya kuma rafi ne na kogin Niger. Tushen kogin yana kusa da Funtua a kudancin jihar Katsina, kimanin 275 kilometres (171 mi) a mike tsaye daga Sokoto. Ta bi ta arewa maso,yamma ta wuce Gusau a jihar Zamfara, inda madatsar ruwa ta Gusau ta samar da tafki mai wadata garin ruwa. A can kasa kogin ya shiga jihar Sokoto inda ya wuce ta Sokoto ya hade da kogin Rima sannan ya juya kudu ya bi ta Birnin Kebbi a jihar Kebbi. Kimanin 120 kilometres (75 mi) kudu da Birnin Kebbi, ya isa mahadarsa da kogin Neja.
Kogin Sokoto | |||||
---|---|---|---|---|---|
kogin | |||||
Bayanai | |||||
Mouth of the watercourse (en) | Nijar | ||||
Tributary (en) | Kogin Rima da Gaminda (en) | ||||
Drainage basin (en) | Niger Basin (en) | ||||
Ƙasa | Najeriya da Nijar | ||||
Wuri | |||||
|
Sokoto | |
---|---|
General information | |
Tsawo | 600 km |
Labarin ƙasa | |
Tsarin Daidaiton Labarin Kasa | 11°24′37″N 7°18′28″E / 11.410175°N 7.307778°E |
Kasa | Najeriya da Nijar |
Hydrography (en) | |
Tributary (en) |
duba
|
Ruwan ruwa | Niger Basin (en) |
River mouth (en) | Nijar |
Filayen da ke kewaye da kogin ana noma su sosai kuma ana amfani da kogin a matsayin tushen ban ruwa. Kogin kuma muhimmin hanyar sufuri ne. Dam din Bakolori, kimanin kilomita 100 kilometres (62 mi) daga sama daga Sokoto, babban tafki ne a kogin Sokoto. Ya yi tasiri sosai a kan noman rafin da ke ƙasa.[1]
Manazarta
gyara sashe- ↑ Akané Hartenbach and Jürgen Schuol (October 2005). "Bakolori Dam and Bakolori Irrigation Project – Sokoto River, Nigeria" (PDF). Eawag aquatic research institute. Retrieved 2010-01-10.