Madatsar Ruwa ta Gusau

madatsar ruwa a kogin Sokoto

Dam din Gusau tana da tafki a kogin Sokoto kusa da Gusau, babban birnin jihar Zamfara a Najeriya. Wannan madatsar tana ba da ruwa ga birni da maƙwabta. A shekarar 2006, madatsar ruwan ta ruguje, inda ta kashe mutane kimanin 40 tare da lalata sada da gidaje 500.

Madatsar Ruwa ta Gusau
Wuri
Geographical location Kogin Sokoto
Coordinates 12°08′41″N 6°40′15″E / 12.14483°N 6.67089°E / 12.14483; 6.67089
Map
Kogin Sokoto, Gusau a kudu maso gabas

karfin Dam

gyara sashe

Dam din bai isa ya biya bukatun gida a lokutan fari ba. A watan Janairun 2001, Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmed Sani Yerima ya gana da Ministan Albarkatun Ruwa na Tarayya, Mohammed Bello Kaliel, ya shaida masa cewa Dam din Gusau zai iya bushewa nan ba da dadewa ba, inda ya nemi Gwamnatin Tarayya ta mika ruwa daga Dam din Bakolori zuwa Gusau. Ministan ya ce gwamnatin tarayya ta dukufa wajen samar da ingantaccen ruwa ga daukacin ‘yan Najeriya, kuma nan ba da jimawa ba za ta samar da tallafi ga jihohin, tare da baiwa Gusau fifiko.

A watan Yunin shekarar 2002, wasu ƙungiyoyin biyu a jihar Zamfara sun kai karar hukumar yaki da cin hanci da rashawa mai zaman kanta (ICPC), bisa zargin Ahmed Sani Yerima da karkatar da kudaden gwamnatin tarayya. Gwamnatin jihar dai ta yi ikirarin inganta, yaye da kuma gyara wani kaso na barikin Gusau da ya ruguje kan kudi Naira miliyan 14.2, da farfado da Barrage a kan Naira miliyan 92 da kuma kwance tashar Dam din Gusau kan Naira miliyan 1.8. Koyaya, ba a yi wani abin godiya ba.

2006 rugujewa

gyara sashe

Wani bala'i ya faru a ranar Asabar 30 ga watan Satumban 2006, lokacin da madatsar ruwa ta ruguje bayan da ruwa ya mamaye. Mutane kimanin 40 suka mutu tare da lalata gidaje kusan 500, kuma mutane sun rasa muhahallansu kimanin 1,000. Hakan ya biyo bayan mamakon ruwan sama mai tsanani da aka tabka a yankin, wanda aka shafe kwanaki biyu anayi. Baya ga hasarar gidaje da kuma lalacewa, ruwan yayi sanadiyyar lalata filayen noma da dama da aka kusa girbi, tare da mutuwar daruruwan dabbobi. Kazalika dam din, ya lalata wata gada da ta hada garin da arewacin jihar Zamfara. Kimanin mutane 700 ne aka tsugunar da su na wani dan lokaci a wata makarantar sakandare da ke kusa da yankin Birnin Ruwa, inda kungiyar agaji ta gaggawa, Nigerian Red Cross ta ba da taimako. Ruwan ya gurbace rijiyoyin ruwan sha. Hatsarin ya faru ne bayan da kofofin sluice suka kasa aiki, lamarin da ya sa ruwa ya mamaye dam ɗin, in ji ma’aikacin hukumar ruwa ta Zamfara .

Bayan rugujewar dam din, mazauna garin da dama sun koma amfani da ruwan rafi. Masu sayar da ruwa sun ninka farashinsu, inda suke sayar da Jarka mai lita 25 akan Naira 50 idan aka kwatanta da N20 a da.

Ci gaba daga baya

gyara sashe

A watan Maris din shekarar 2007, gwamnatin tarayya ta fitar da naira biliyan 2.4 domin gyaran madatsar ruwa ta Gusau. A cikin watan Mayun 2007 gwamnatin jihar Zamfara ta ce suna ba da fifiko mafi girma wajen tabbatar da cewa an kiyaye ruwa a madatsar ruwa, gyara matatun ruwa, samar da kayan aiki na zamani a tashoshin famfo, da bunkasa hanyoyin rarraba ruwa.

A watan Janairun 2010 wata kungiya mai zaman kanta a Zamfara mai suna Concerned Citizens ta roki Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati (EFCC) da ta binciki tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmad Sani Yarima, kan wasu makudan kudade da suka hada da rancen Naira biliyan daya na gyaran madatsar ruwa ta Gusau.

12°08′41″N 6°40′15″E / 12.14472°N 6.67083°E / 12.14472; 6.67083Page Module:Coordinates/styles.css has no content.12°08′41″N 6°40′15″E / 12.14472°N 6.67083°E / 12.14472; 6.67083