Siyudi
Jalal-Addin Al-Suyuti ko Imam Al-Suyuti wanda aka sani da ma'abocin jalalaini an haife shi ne a watan Rajab ranar Asabar shekara ta dari takwas da arba'in da hudu bayan hijira 849AH, wanda yayi daidai da 3 gawatOn oktoban shekara ta alif dari hudu da arba'in da biyar 1445 MD, a garAn al-kahira. Mahaifiar sa ta kasanBe Balarabiya ce mahaifin sa kuma yazo garin suyud dadaga bagadaza. Sunan sa Abdurrahman dan Abuabakar dan Muhammadul kubriyu dan garin suyud, Mahaifin suyudi yakasance yan koyarwa a masallaci da wasu da'irorin ilimi. Amma mahifin sa yamutu alokacin shekarun sa basufi 5 zuwa 6. Yarayu yana maraya, kuma yayi ta kokari har yasamu haddar Al-kur'ani, ya haddace shi alokacin da yake baifi da shekaru 8 ba. Sannan yahaddace wasu littattan a wannan kananun shekarun sa kamar umdatu(العمدة), Manhajul fikihi wal usul(منهاج الفقه والأصول), Alfiyyatu ibni Malik(ألفية ابن مالك), hakkan ya kara masa sani da kuma ilimi daga wuraren malamai masu yawa musamman daga daliban mahaifin sa kamar kamal dan himamu Al-hanki daya daga cikin manya-manyan malaman zamanin sa.
Sannan yayi tafiye tafiyen neman ilimi zuwa yankin larabawa sham, yaman, indiya, da maroko. Yakoyi ilimai masu yawa waddan da suka hadda da fikihu a mazahobi, Hadsi, Tauhidi, Tarihi, Falsafa, Hisabi, Likitanci da ilimin lokota, ya fara shari'ar imamu Shafi`i alokacin yana shekara 18 a masallacin da mahaifinsa ya rasu, sannan a shekarata 1486 sarki Qaitbay ya naɗa shi amatsayin babban malamin sufaye a wata zawiyya da ke a khanqah. Suyudi shima sufine wanda yake bin darikar shazaliya
Hakkannan anyiwa suyudi lakabi da mujaddadi na kari 9 H.hakkan yahaifar da kuma rashin jituwa a tsakanin malamai da gwamnati, sannan wata rashin jituwa da aka samu a kan kudin tafida zawiyya , sai suyudi ya koma wani tsubiri a kasar Ruwanda a shekarata 1501. Imamu suyudi ya rasu 18 ga oktoba a shekara ta 1505. Ya wallafa littafai da yawa kaman su Jami'ul hadith, tariq.