Shina Abiola Peller (an haife shi a ranar 14 ga watan Mayu a shekara ta 1976) ɗan kasuwan Najeriya ne, ɗan siyasa, masanin masana'antu, kuma ɗan majalisar wakilai ta ƙasa ta 9. Shi ne shugaba kuma babban jami'in gudanarwa na Aquila Group of Companies da Club Quilox. [1] Shina Peller yana rike da sarautar Ayedero na kasar Yarbawa da Akinrogun na Epe land, Lagos [2]

Shina Peller
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

21 ga Yuni, 2022 -
mamba a majalisar wakilai ta Najeriya

11 ga Yuni, 2019 - 17 ga Yuni, 2022
District: Iseyin/Itesiwaju/Kajola/Iwajowa
Rayuwa
Haihuwa Iseyin (birni), 14 Mayu 1974 (49 shekaru)
ƙasa Najeriya
Ƴan uwa
Abokiyar zama Ayọ̀bọ́lá (en) Fassara
Karatu
Makaranta Jami'ar Takanolaji na Ladoke Akintola
Harsuna Yarbanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Fage gyara sashe

Shina Abiola Peller da ne ga Alhaja Silifat da Farfesa Moshood Abiola Peller.[3] Ya taso a gidan musulmai.Ya samo asali ne daga garin Iseyin dake jihar Oyo a kudu maso yammacin Najeriya.Ya karanta Chemical Engineering a Ladoke Akintola University of Technology, Ogbomosho, Nigeria, inda ya sami digiri na farko a shekara ta 2002.[4] Bayan haka, ya sami digiri na biyu a fannin kasuwanci kuma daga Jami'ar Fasaha ta Ladoke Akintola a shekara ta 2013. Ya yi aiki a jihar Abia a shekarar 2003 don cika wajabcin hidimar bautar kasa na shekara daya da ake bukata ga duk ‘yan Najeriya da suka kammala karatunsu.[5]

Sana'ar siyasa gyara sashe

Peller dan jam’iyyar All Progressive Congress ne,[6] kuma ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara a karkashin jam’iyyar All Progressive Congress a matsayin dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar tarayya ta Iseyin/Itesiwaju/Iwajowa/Kajola a jihar Oyo.[7][8][9]

A ranar 5 ga watan Oktoba a shekara ta 2018, Shina Peller ya lashe zaben fidda gwani na dan takarar majalisar wakilai ta tarayya mai wakiltar mazabar lseyin/ltesiwaju/Kajola/lwajowa a jam’iyyar APC a babban zaben shekara ta 2019 kuma ya lashe kujerar. Ya lashe kujerar majalisar wakilai a mazabarsa a ranar 23 ga watan Fabrairu a shekara ta 2019.[10][11] A yanzu haka yana neman takarar majalisar dattawan Najeriya a karkashin inuwar Accord Party.[12]

Manazarta gyara sashe

  1. Shina Peller Biography https://www.naija.ng/1120204-shina-peller-biography.html#1120204
  2. "2023: We shall donate our hard earned money to support you, group tells Shina Peller". Vanguard News (in Turanci). 2021-12-29. Retrieved 2022-02-22.
  3. "Ayedero Shina Peller: The 'King of night life' now 'King of hearts'". Tribune Online (in Turanci). 2021-08-27. Retrieved 2022-03-18.
  4. "Shina Peller: 10 things you didn't know about Quilox boss". 25 August 2015.
  5. Henry. "Who is Shina Peller? All you need to know about the son of a magician". Daily Advent. Retrieved 26 January 2019.
  6. "Why I want to serve my people – Shina Peller". Archived from the original on 2018-09-12. Retrieved 2022-12-09.
  7. Olowookere, Dipo. "Shina Peller Flags off Campaign for House of Reps Seat".
  8. "Alaafin endorses Shina Peller for House of Reps". 25 August 2018.
  9. Abubakar, Muritala (June 2018). "Shina Peller declares intention to contest for house of reps in 2019".
  10. "Nightclub Owner Shina Peller Wins APC House of Reps Ticket". 5 October 2018.
  11. Okogba, Emmanuel (24 February 2019). "Shina Peller wins Iseyin Federal Constituency seat".
  12. Elijah, Ima (2022-07-05). "Shina Peller secures Accord Party ticket for Oyo North senatorial district". Pulse Nigeria (in Turanci). Retrieved 2022-07-14.