Shehu Hassan Kano

Jarumin kannywood

Shehu Hassan Kano (An haifeshi ranar 25 ga watan Mayun sheka ta 1968). Kwararren ɗan wasan fina-finan hausa ne a masana'antar fim ta Kannywood, kuma ɗan jarida wanda ya bada gaggarumar gudummawa a masana'antar shirya fina-finan dake da hedikwatar ta a birnin Kano, yafi taka rawa a ɓangaren fitowa a matsayin uba a cikin shirin film ɗin Hausa.

Shehu Hassan Kano
Rayuwa
Haihuwa Fagge, 25 Mayu 1968 (56 shekaru)
ƙasa Najeriya
Sana'a
Sana'a jarumi

An haifi Shehu Hassan Kano a ranar 25 ga watan Mayu shekara ta 1968, a unguwar Fagge dake jihar Kano, Najeriya.

Sana'ar fim

gyara sashe

Shehu Hassan Kano ya fito a fina-finai da dama, da suka wuce a lissafa su. Suna daga cikin jarumai na farko a duniyar wasan Hausa. Ga wasu kaɗan daga cikin su:

  • Kaddara ta Riga Fata,
  • Saudatu (iya tama Multimedia)
  • Hauwa (NB Entertainment)
  • Jurumta
  • Ƙara'i
  • Gidan Farko
  • Duniyar mu
  • Labarina
  • Ba'asi, da dai sauran su.

[1] [2]

Manazarta

gyara sashe