Salisu Abubakar Maikasuwa ma'aikacin Najeriya ne wanda ya yi aiki a matsayin magatakarda na majalisar dokokin Najeriya.[1]

Salisu Abubakar Maikasuwa
Rayuwa
Haihuwa Keffi, 4 ga Maris, 1958 (66 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Makaranta Jami'ar, Jos
Jami'ar Ahmadu Bello
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa

Rayuwar farko

gyara sashe

Salisu Abubakar Maikasuwa wanda aka haifa a ranar 4 ga watan Maris, shekara ta 1958 da ga Abubakar da Fatima Maikasuwa na masarautar Keffi .

Abubakar maikasuwa ya halarci makarantar firamare ta Abdu Zanga, Keffi daga inda ya sami takardar shedar kammala makarantar sa ta farko (FSLC) a cikin shekara ta 1970. Ya samu takardar shedar kammala karatu a Makarantar Afirka ta Yamma ne a shekara ta 1975, bayan ya shiga makarantar Kuru ta gwamnati a Jihar Filato ta yanzu a shekara ta 1971. Ya yi karatun sa ne a Makarantar Koyon Karatun Firamare, Zariya, sannan ya samu takardar shedar karatun boko a makarantar kuma nan da nan ya samu shiga Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya samu Digiri na farko a kan ilimin zamantakewar al’umma a shekara ta 1980. Ya sami digiri na biyu a fannin Gudanar da Jama'a da nazarin siyasa, Jami'ar Jos a shekara ta 1983.

Kyauta da Girmamawa

gyara sashe

Manazarta

gyara sashe

Kara karantawa a http://expressng.com/2015/06/nass-clerk-salisu-maikasuwa-meet-man-who-crowned-bukola-saraki-as-senate-president/#kfBcMTI0qIvjc0Yx.99

  1. http://expressng.com/2015/06/nass-clerk-salisu-maikasuwa-meet-man-who-crowned-bukola-saraki-as-senate-president/