Salih bin Abdullah al Humaid
Sāliḥ ibn `Abd Allāh Ibn Humayd (Larabci: صالح بن عبد الله ابن حميد, Saleh bin Abdullah bin Humaid; an haife shi shekara ta, alif ɗari tara da arba'in da tara (1949) [1] limamin Saudiyya ne kuma ɗan siyasa. A halin yanzu yana daya daga cikin limamai tara na babban masallacin Makkah. Ya kuma kasance memba na Majalisar Saudi Arabiya tun shekarar, 1993 kuma ya rike Kakakin Majlis al Shura daga watan Fabrairu shekarar, 2002 zuwa watan Fabrairu shekarar, 2009.
Salih bin Abdullah al Humaid | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 10 Mayu 1947 (77 shekaru) | ||
ƙasa | Saudi Arebiya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Q20412522 | ||
Kyaututtuka | |||
Mamba |
International Islamic Fiqh Academy (en) Council of Senior Scholars (en) |
Salih Humaid memba ne a Majlis al Shura (Majalisar Tuntuba ta Saudiyya ) tun daga shekarar, 1993 kuma shugaban Majlis al Shura daga watan Fabrairun shekarar, 2002 zuwa watan Fabrairun shekarar, 2009. [2] A halin yanzu limamin masallacin Harami ne (Masallacin Harami na Makkah). Shi ma memba ne a Kwalejin Harshen Larabci da ke Makkah, [3] kuma Shugaban Makarantar Fiqhu ta Duniya da ke Jeddah.
Ya lashe lambar yabo akan Hidimatawa Musulunci a shekarar, 2016 daga lambar yabon da Sarki Faisal ya bayar. Daga cikin wasu lambobin yabon daban-daban.
Dan Abdullahi bn Humaid ne.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Dr. Saleh bin Abdullah bin Humaid
- ↑ The Shura Council of Kingdom of Saudi Arabia - A Brief History
- ↑ معالي الشيخ الدكتور/ صالح بن عبدالله بن حميد Archived 2022-08-02 at the Wayback Machine. Official website of the Academy, 9 February 2015. Accessed 8 November 2016.