Sadiq Abdulkarim Abdulrahman
Sadiq Abdulkarim Abdulrahman likita ne kuma ɗan siyasan Libya wanda ya yi aiki a matsayin mataimakin firaminista na farko tsakanin 14 ga watan Nuwamba shekara ta 2012 da kuma ranar 29 ga watan Agusta shekara ta 2014.
Sadiq Abdulkarim Abdulrahman | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | 1966 (57/58 shekaru) |
Sana'a | |
Sana'a | likita da ɗan siyasa |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Rayuwar farko da ilimi
gyara sasheAn haifi Abdulrahman a wajajen shekara ta 1966. Ya sami digiri na farko a babban aikin tiyata a shekarar 1993. Sannan ya sake karatun digiri na biyu a fannin likitanci a shekara ta 2001 sannan ya sake yin karatun digirin-digirgir a fannin likitanci a shekara ta 2005.
Ayyuka
gyara sasheAbdulrahman yayi aiki a matsayin likita a asibitocin gwamnati da kuma asibitoci masu zaman kansu. Sannan ya yi aiki a matsayin mataimakin firaminista a gwamnatin rikon kwaryar Libya . An nada shi mataimakin firaminista na farko a ranar 14 ga watan Nuwamba shekara ta 2012 zuwa majalisar ministocin karkashin jagorancin Ali Zidan . Abdulrahman ya kuma rike mukamin mukaddashin ministan cikin gida na wani lokaci. A ranar 29 ga watan Janairun shekara ta 2014 ya tsere daga wani yunƙurin kashe shi ba tare da rauni ba a cikin Tripoli .
Abdulrahman na wa’adin mataimakin firaminista ya kare ne a ranar 29 ga watan watan Agustan shekara ta 2014.