Rashid Seidu
Rashid Seidu (an haife shi a ranar 14 ga watan Satumban 1995) ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne, ɗan ƙasar Ghana wanda ke taka leda a matsayin mai tsaron gida. A cikin shekarar 2015, ya sami kira na ƙasa kuma ya kasance memba na Ghana U23 a 2015 All-Africa Games. [1]
Rashid Seidu | |||||||||||||||||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
Rayuwa | |||||||||||||||||||||||
Haihuwa | Accra, 14 Satumba 1995 (29 shekaru) | ||||||||||||||||||||||
Sana'a | |||||||||||||||||||||||
Sana'a | ɗan wasan ƙwallon ƙafa | ||||||||||||||||||||||
|
Aikin kulob
gyara sasheSeidu ya rattaba hannu a ƙungiyar ƙwararru ta Asante Kotoko, a ranar 3 ga watan Janairun 2011. Kuma ya koma kulob ɗin AS Douanes na Nijar (Niger) inda ya ƙulla kwantiragi na shekara tare da zaɓin sabunta shi a ƙarshen kakar wasa ta bana amma ya ɗan yi jinkiri[2].
Daga bisani ya koma Bechem United a cikin watan Yulin 2013, inda ya rattaɓa hannu kan shekaru biyu da kulob ɗin gasar Premier ta Ghana[3][4].
A cikin shekarar 2015, Seidu ya koma kulob ɗin gasar Premier ta Ghana Wa All Stars yanzu Legon Cities kan yarjejeniyar shekaru huɗu. A cikin watan Mayun 2020, ya shiga Inter Allies.
Ayyukan ƙasa da ƙasa
gyara sasheA cikin watan Janairun 2015 an gayyace shi don shiga cikin tawagar ƙasa ta U23 a wasannin share fage na Wasannin Afirka duka.
Girmamawa
gyara sasheKulob
gyara sasheAsante Kotoko
- Gana Premier League: 2011-2012
Bechem United
- Ghana Super Cup: 2011-2012
Wa All Stars
- Gana Premier League: 2016
- Gana Super Cup: 2017
Manazarta
gyara sashe- ↑ https://www.flashscore.com/player/seidu-rashid/tENH6OHj/
- ↑ https://www.ghanaweb.com/GhanaHomePage/SportsArchive/GPL-transfer-wrap-Know-the-players-each-club-signed-508721
- ↑ https://newsghana.com.gh/gfa-call-players-black-meteors/
- ↑ https://www.modernghana.com/sports/626649/kotoko-coach-david-duncan-admits-difficult-win-over-bechem.html
Hanyoyin haɗi na waje
gyara sashe- Rashid Seidu at FootballDatabase.eu