An haifi Rahma Sherif Abdul-Majid a shekarar 1980 a Agege, jihar Lagos, Najeriya, mahaifinta Balarabe ne kuma mahaifiya Hausa Fulani. Ta fara karatun Alkur'ani a gidan mahaifinta kuma ta shiga makarantar firamare tana 'yar shekara tara. Ta samu difiloma a shari’ar Shari’a a 2001. Ta wuce zuwa shahararriyar Jami’ar Al-azhar da ke Alkahira don karatun digirin farko a inda ta samu digirin BA a tarihi da karatun duniya. Ta fara rubutu a 1996 kuma ta buga littattafai sama da ashirin. Tana cikin kungiyoyi masu zaman kansu da kungiyoyi masu wayar da kai kuma a yanzu haka ita ce shugabar kungiyar Mace Mutum, wacce take karkashin kungiyar marubutan matan Hausawa a Najeriya.

Rahma Abdulmajid
Rayuwa
Haihuwa Agege, 1980 (43/44 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Harsuna Turanci
Sana'a
Sana'a marubuci

Manazarta

gyara sashe