Rahat Indori
Rahat Indori (an haifeshi a ranar 1 ga watan Janairun 1950 kuma ya mutu a ranar 11 ga watan Augustan 2020) ya kasance mawakin waƙoƙin masana'antar finafinai ta Bollywood na Indiya, kuma mawaƙin Urdu. Ya kuma kasance tsohon farfesa a yaren Urdu kuma mai zane. Ya kasance malamin harshe a Jami'ar Devi Ahilya, Indore . A matsayinsa na mai shirya fim, fitattun ayyukan da ya yi sun haɗa da Khuddar, Mission Kashmir da Meenaxi: Tatsuniyoyin Garuruwa Uku . An haifi Indori a cikin Indore, Madhya Pradesh . Indori ya mutu a ranar 11 ga watan Agusta 2020 a wani asibiti a cikin Indore, a sakamakon annobar COVID-19, yana da shekaru 70. An gwada shi tabbatacce don kamuwa da cutar daren da ya gabata.
Rahat Indori | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Indore, 1 ga Janairu, 1950 |
ƙasa |
Indiya Dominion of India (en) |
Mutuwa | Indore, 11 ga Augusta, 2020 |
Yanayin mutuwa | (Koronavirus 2019) |
Karatu | |
Makaranta |
Barkatullah University (en) Madhya Pradesh Bhoj Open University (en) |
Sana'a | |
Sana'a | lyricist (en) , mai rubuta waka, maiwaƙe da marubuci |
Imani | |
Addini | Musulunci |
IMDb | nm0408534 |
rahatindori.com |