Princewill Ogbogbula (an haife shi ranar 18 ga watan Satumban 1970) shi ne kwamishinan ci gaban matasa na yanzu a majalisar zartarwa ta jihar Ribas.[1] Gwamna Ezenwo Nyesom Wike ne ya naɗa shi muƙamin a cikin shekarar 2015.

Prince Ogbogbula
Ɗan Adam
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Suna Prince (en) Fassara
Shekarun haihuwa 18 Satumba 1970
Sana'a ɗan siyasa
Ilimi a University of Port Harcourt (en) Fassara da Jami'ar jihar Riba s
Ɗan bangaren siyasa Rivers State People's Democratic Party (en) Fassara

Rayuwar farko da ilimi gyara sashe

An haife shi a Garin Ubio da ke ƙaramar hukumar Ahoada ta Yamma, ya samu shaidar kammala karatunsa na babbar makarantar sakandare ta Afirka ta Yamma a cikin shekarar 1988 a Makarantar Sakandaren Al’umma ta Erema. A cikin shekara ta 1995, ya sauke karatu daga Jami'ar Fatakwal da BA a Marketing. Sannan ya sami digirin digirgir a fannin kasuwanci a Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Ribas a shekarar 2000.[1]

Sana'a gyara sashe

Ci gaban matasa gyara sashe

Ya shiga Majalisar zartarwa ta Wike a matsayin Kwamishinan Ci gaban Matasa a cikin watan Disamban 2015.[2]

Wasu ofisoshin da aka gudanar gyara sashe

Ogbobula ya riƙe wasu muƙamai kamar:

  • Shugaban jam'iyyar LGA (Ahoada West PDP) manajan gudanarwa na kungiyar (Orashi Energy Nig Ltd) - (Paun Nig Ltd)
  • Manazarcin kasuwa da manajan ci gaban kasuwa - Bonny Allied Industries Ltd (masu yin Rock Cement)
  • Wakilin tallace-tallace (yankunan kudu-kudu & kudu maso gabas) - Bonny Allied Industries Ltd (masu yin Rock Cement)
  • Manajan kulob - Air Assault Golf Club, Port Harcourt

Duba kuma gyara sashe

  • Jerin mutanen jihar Ribas
  • Ƙarfafa matasa

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 "Kwafin ajiya". Archived from the original on 2017-05-10. Retrieved 2023-04-10.
  2. http://www.thetidenewsonline.com/2016/05/04/rsg-recommits-to-sifmis-implementation/