Preye Oseke
Preye Influence Goodluck Oseke (an haife shi a ranar 27 ga watan Mayu 1976) ɗan siyasan Najeriya ne kuma ɗan majalisar wakilai ta tarayya a majalisar wakilai ta ƙasa ta 9. [1]
Preye Oseke | |
---|---|
Rayuwa | |
ƙasa | Najeriya |
Sana'a | |
Sana'a | ɗan siyasa |
Imani | |
Jam'iyar siyasa | All Progressives Congress |
Tarihi da ilimi
gyara sasheAn haifi Oseke a shekarar 1967 a Ogboinbiri, ƙaramar hukumar Ijaw ta kudancin jihar Bayelsa. Ya fara karatun firamare ne a shekarar 1983 a makarantar Apoi Clan Central da ke garin Ogboinbiri inda ya samu shaidar kammala karatunsa na farko a shekarar 1987. [2] Ya shiga makarantar Bishop Dimieari Grammar School (BDGS) Yenagoa domin yin karatunsa na sakandire kuma ya gama da Senior Secondary School Certificate, SSCE a 1993. Ya samu digirin farko a fannin harkokin gwamnati a jami'ar Fatakwal a shekarar 2012.
Aikin siyasa
gyara sasheAn zaɓi Oseke a matsayin ɗan majalisar wakilai ta tarayya daga yankin kudancin Ijaw tarayya kan tikitin jam’iyyar All Progressives Congress a shekarar 2019.[3] An ƙalubalanci zaɓensa a kotu amma ya sake tabbatar da cewa shi ne ya lashe zaɓen. A shekarar 2021, lauyansa, Andrew Chukwuemerie wani farfesa a fannin shari’a kuma Babban Lauyan Najeriya, SAN ya kai karar Oseke bisa rashin biyan kuɗaɗen shari’a na shari’ar zaɓen shekarar 2019. [4] Oseke ya kasance mamba a kwamitin majalisar kan harkokin ƙasashen waje a majalisa ta 9. [5]
A shekarar 2022, ya lashe zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar APC da kuri’u 16,511 don sake tsayawa takara a karo na biyu a majalisar wakilai. [6] A zaɓen ranar 25 ga watan Fabrairun 2023, ɗan takarar jam'iyyar People's Democratic Party (PDP) ya doke shi da kuri'u 13,992 yayin da Oseke mai ci ya samu kuri'u 12,992.
Manazarta
gyara sashe- ↑ Daily Post Staff (2019-07-02). "Bayelsa guber election: Oseke speaks on 'planning' to succeed Dickson". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-05-05.
- ↑ Alexis, Silas Diton (2022-02-15). "See Intimidating Profile of Hon. Preye Influence Goodluck Oseke, the Most outstanding Federal Lawmaker of the Year". Naija Live Tv (in Turanci). Retrieved 2023-05-05.
- ↑ Nigeria, News Agency of (2023-04-16). "PDP, APC win supplementary elections in Bayelsa". Peoples Gazette (in Turanci). Retrieved 2023-05-05.
- ↑ "Professor Drags Bayelsa Rep, Oseke to Court over Outstanding Professional Fees – THISDAYLIVE". www.thisdaylive.com. Retrieved 2023-05-05.
- ↑ "Reps committee appeals to commission to spend 2019 budget allocation". The Guardian Nigeria News - Nigeria and World News (in Turanci). 2019-10-28. Retrieved 2023-05-05.
- ↑ James, Akam (2022-05-28). "APC Primaries: Oseke, Sunny-Goli, 3 others win Reps tickets in Bayelsa". Daily Post Nigeria (in Turanci). Retrieved 2023-05-05.