Jaridar Peoples Daily jarida ce dake Najeriya. An ƙaddamar da ita a matsayin za'a dinga wallafa labarai mako-mako a cikin watan Nuwamban 2008, kuma ta dawo tana wallafa labarai kullun a cikin Nuwamba 2009.[1][2]

Peoples Daily
Bayanai
Iri takardar jarida
Ƙasa Najeriya
Tarihi
Ƙirƙira 2008

Tarihin Kafata

gyara sashe

An gabatar da jaridar Peoples Daily a hukumance a wani biki a Abuja a watan Maris 2010.Shugaban kwamitin gudanarwar gidan jaridar shine Malam Wada Abdullahi Maida. A wajen bikin, Malam Ismaila Isa ya bayyana cewa, duk da jita-jitar da ake yaɗawa, jaridar Peoples Daily ba mallakin tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar ba ne. Maimakon haka, gidan jaridar mallakin sama da ƙwararrun kafofin watsa labarai 40.

A cikin watan Disambar shekarar 2009, jami’an hukumar tsaro ta farin kaya sun kama editan jaridar, Malam Ahmed Shekarau, bisa wani rahoto kan lafiyar shugaba Umaru Yar’adua mai fama da rashin lafiya. Daga baya Shekarau ya bar Peoples Daily ya koma gidan jaridar Daily Trust a matsayin Janar Manaja.

Manazarta

gyara sashe
  1. "Daily newspaper launched". Charles McGhee Media. Archived from the original on 2012-03-24. Retrieved 2011-05-14.
  2. "Thomson Foundation helps launch new Nigerian daily newspaper". Thomson Foundation. December 9, 2009. Archived from the original on June 14, 2011. Retrieved 2011-05-14.