Paul Antoine Bohoun Bouabré (9 ga watan Fabrairu, 1957-Janairu 10, 2012), ɗan siyasan Ivory Coast ne kuma masanin tattalin arziki, kuma amintaccen tsohon shugaba Laurent Gbagbo.[1] Mataimakin Farfesa ne a fannin tattalin arziki kuma masanin tattalin arziki, ya kasance ministan tattalin arziki da kuɗi da kuma ministan tsare-tsare da raya ƙasa a gwamnatocin Soro, mukamin da ya taba rikewa kenan a gwamnatin Banny.[2]

Paul Antoine Bohoun Bouabré
Minister of the Economy and Finance of Ivory Coast (en) Fassara

ga Janairu, 2001 - Disamba 2005
Mamadou Koulibaly (en) Fassara - Charles Konan Banny
Rayuwa
Haihuwa 9 ga Faburairu, 1957
ƙasa Ivory Coast
Mutuwa Jerusalem, 10 ga Janairu, 2012
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a Mai tattala arziki da ɗan siyasa
Bohoun Bouabré a cikin 2004

Tarihin Rayuwa gyara sashe

Lokacin da ya isa mukamin Ministan Tattalin Arziki da Kuɗi, bai ƙarfafa kwarin gwiwa ba. amma yanzu an gane shi a matsayin babban mai tsara tsarin kula da tattalin arzikin Ivory Coast. Yayin da ƙasar ke cikin yaƙin basasa, ya yi nasarar kula da yanayin rayuwa, da tabbatar da biyan jami'ai, basussukan ƙasa da kuma dawo da masu ba da taimako a Cote d'Ivoire. Ya kara albashin jami’an tsaro (domin magance cin hanci da rashawa), duk ba tare da lamuni ba. A cikin shekarar 2005 ya "sanar da daftarin kasafin Kuɗi na CFAFl,734.97bn, yana mai cewa za a samar da adadin ne musamman daga albarkatun cikin gida."[3]

A shekara ta 2004, shi da Hubert Oulaye sun rattaba hannu kan wata doka mai lamba 1437 wacce ta bayyana cewa duk takardar neman iznin kwangilar dole ne Ministan Ayyuka ya amince da shi. A shekarar 2005 aka naɗa shi ministan tsare-tsare da raya ƙasa, sannan aka sake naɗa shi a shekarar 2007. A cikin shekarar 2006, ya nuna aniyarsa ta zama gwamnan BCEAO.

Bohoun zai zama Gwamnan Babban Bankin Yammacin Afirka, don maye gurbin Charles Konan Banny, amma a cikin watan Janairu 2008, Laurent Gbagbo da sauran shugabannin Afirka ta Yamma sun zaɓi Philippe-Henri Dacoury-Tabley. Ya rasu ne a watan Janairun 2012 a birnin Kudus bayan fama da ciwon koda.[4]

Manazarta gyara sashe

  1. Besada, Hany (1 September 2009). From Civil Strife to Peace Building: Examining Private Sector Involvement in West African Reconstruction. Wilfrid Laurier Univ. Press. p. 45. ISBN 978-1-55458-052-1. Retrieved 16 July 2012.
  2. "Paul-Antoine Bohoun Bouabré : vie et mort d'un patriote ivoirien". Le Nouveau Courrier (in French). 12 January 2012. Retrieved 16 July 2012.CS1 maint: unrecognized language (link)
  3. Africa research bulletin: Economic, financial, and technical series. Blackwell. 1 January 2005. Retrieved 16 July 2012.
  4. Mieu, Baudelaire (11 January 2012). "Côte d'Ivoire : décès à Jérusalem de Paul-Antoine Bohoun Bouabré". Jeune Afrique (in French). Archived from the original on 23 March 2021. Retrieved 5 July 2021.CS1 maint: unrecognized language (link)