Pally Iriase
Pally Isumafe Obokhuaime Iriase (an haife shi a ranar 19 ga watan Janairun 1955) tsohon ɗan majalisar wakilan Najeriya ne [1] kuma tsohon mataimakin kakakin majalisar dokokin jihar Edo. [2]
Pally Iriase | |||
---|---|---|---|
| |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 19 ga Janairu, 1955 (69 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa da accountant (en) |
Ilimi
gyara sasheIriase ya halarci makarantar Anglican Grammar School Otuo kafin ya wuce Jami'ar Najeriya, Nsukka don samun digiri na farko a shekarar 1982. [3] A shekarar 1988, ya sami digiri na biyu a fannin Accounting a Jami’ar Legas. [3]
Sana'a
gyara sasheIriase ya yi aiki a matsayin babban mai binciken cikin gida a Jami'ar Jihar Bendel yanzu Ambrose Alli University Ekpoma (1982-1992) kafin ya koma duniyar kamfanoni a matsayin mai kula da yankin Omega Bank (1995-1998).
Siyasa
gyara sasheA shekarar 1999, Iriase ya tsaya takara kuma ya lashe zaɓen majalisar dokokin jihar Edo inda 'yan majalisar suka zaɓe shi mataimakin shugaban majalisar. A shekarar 2003, ya bar takarar shugaban ƙaramar hukumar Owan ta Gabas kuma ya yi nasara. Ya taɓa zama shugaban kungiyar Ƙananan Hukumomin Najeriya (ALGON) reshen Jihar Edo (2003-2007) sannan ya zama mataimakin shugaban, ALGON, Najeriya. An naɗa shi sakataren gwamnatin jihar Edo a shekarar 2008 kuma ya yi aiki har zuwa shekarar 2011.
A shekarar 2011, Iriase ya tsaya takara a babban zaɓe kuma ya yi nasara a matsayin ɗan majalisar wakilai, mai wakiltar mazaɓar Owan ta gabas da ta yamma kuma an sake zaɓe a shekarar 2015 yana yin wa'adi biyu na shekaru huɗu. [4]
A shekarar 2018 ne dai rahotanni suka ce jam'iyyar APC Ward Tara (9) a ƙaramar hukumar Owan ta Gabas ta jihar Edo ta kore shi daga jam'iyyar, a wata sanarwa da Zuberu Shabah da kuma Theophilus Aigboje, shugaban jam'iyyar da sakatarenta suka sanyawa hannu. Sai dai korar ta fito daga bakin mataimakin shugaban jam’iyyar na jihar Edo ta Arewa, Sunny Okomayin, yana mai cewa kasancewarsa mamba a kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) na Unguwa da Ƙananan Hukumomi ba su da hurumin yin hakan. [5] [6]
Manazarta
gyara sashe- ↑ "Contest for Reps Speaker gets keener". The Guardian Nigeria (in Turanci). 2015-05-01. Retrieved 2022-08-16.
- ↑ "APC House of Reps Primaries Aisowieren, Igbe, Iriase, others emerge winners". Nigerian Observer (in Turanci). 2014-12-08. Retrieved 2022-08-17.
- ↑ 3.0 3.1 "Hon. Pally Iriase biography, net worth, age, family, contact & picture". www.manpower.com.ng. Retrieved 2022-08-20.
- ↑ "LIST - New House of Reps Members for Nigeria's 8th National Assembly". Premium Times Nigeria. 2 May 2015.
- ↑ "Expulsion of Reps deputy chief whip 'nullity' -- APC Chapter". Premium Times Nigeria (in Turanci). 2018-09-25. Retrieved 2022-08-20.
- ↑ "Ward executives disown purported expulsion of Pally Iriase". Vanguard News (in Turanci). 2018-09-27. Retrieved 2022-08-20.