Ousseynou Cavin Diagné (an haife shi ranar 5 ga watan Yunin 1999)[1] ƙwararren ɗan wasan ƙwallon ƙafa ne na ƙasar Senegal wanda ke taka leda a ES Zarzis.

Ousseynou Diagné
Rayuwa
Haihuwa Dakar, 5 ga Yuni, 1999 (25 shekaru)
ƙasa Senegal
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan wasan ƙwallon ƙafa
Hanya
Ƙungiyoyi Shekaru Wasanni da ya/ta buga Ƙwallaye
  Cádiz Club de Fútbol (en) Fassara-
 
Muƙami ko ƙwarewa Mai buga tsakiya

Ya buga wasan ƙwallon ƙafa na matasa don Cádiz CF kuma yana da ɗan wasa kaɗan a Le Mans da Club Brugge II kafin ya koma ƙasarsa ta huɗu ta Turai, ya rattaɓa hannu kan Kristiansund BK a cikin watan Fabrairun 2020.[2] Ya buga wasansa na farko na Eliteserie a cikin watan Yulin 2020 da Bodø/Glimt.[3] A cikin shekarar 2021 ya yi gwaji tare da Raufoss IL, amma ya zauna tare da Kristiansund.[4] Duk da haka an sake shi a ƙarshen watan Mayun 2021.[5]

A duniya, ya kasance memba na tawagar don gasar cin kofin Afrika na U-20 na 2017, gasar cin kofin Afrika na U-20 na 2019 da kuma 2019 FIFA U-20 World Cup.[2]

Manazarta

gyara sashe