Oumarou Sidikou (1937? – 5 ga Afrilun shekarar 2005 [1] ) ɗan siyasan Nijar ne. Ya kasance Mataimakin Gwamnan Babban Bankin na Afirka ta Yamma (BCEAO) [1][2] daga shekarar 1988 zuwa 1993. Ya kasance memba na jam'iyyar National Movement for the Development of Society (MNSD), kuma bayan zaɓen majalisar dokoki na watan Janairun shekarar 1995, wanda kuma kawancen da ya haɗa da MNSD ya lashe, an naɗa Sidikou a matsayin Ministan Jiha mai kula da Masana'antu Ci gaba, Kasuwanci, Masana'antu, da yawon buɗe ido a gwamnatin Firayim Minista Hama Amadou a ranar 25 ga Fabrairun shekarar 1995. [3] An tumɓuke wannan gwamnatin a wani juyin mulkin soja a ranar 27 ga Janairu, shekarata 1996.

Oumarou Sidikou
Member of the National Assembly of Niger (en) Fassara

Rayuwa
Haihuwa N'Dounga, 1938
ƙasa Nijar
Mutuwa Rabat, 5 ga Afirilu, 2005
Karatu
Harsuna Faransanci
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa National Movement for the Development of Society (en) Fassara

Sidikou shi ne mahaifin Fatouma, Aïssa, Aboubakar, Hadizatou, Balkissa, Amadou, Ali, Rokhaya da Mohamed.

An zaɓi Sidikou ga Majalisar Dokoki ta kasa a zaɓen majalisar dokoki na Nuwamban Shekarar 1999 a matsayin ɗan takarar MNSD a Sashen Tillabéri, [4] kuma a cikin wa’adin majalisar da ya biyo baya ya yi aiki a matsayin Shugaban ƙungiyar MNSD ta Majalisar Wakilai da Shugaban Hukumar Kudi.[5] and Presid.[6] An sake zaɓar sa zuwa Majalisar Dokoki ta Kasar a zaɓen majalisar dokoki na Disamba 2004 kuma ya zama Mataimakin Shugaban Ƙasa na farko na Majalisar, amma ya mutu a wani asibiti a Morocco a watan Afrilun 2005. [1]

Manazarta gyara sashe

  1. 1.0 1.1 1.2 "Décès au MAroc du 1er vice-président de l'Assemblée nationale du Niger" Archived 2007-09-26 at the Wayback Machine, aujourdhui.ma, April 8, shekarata 2005 (in French).
  2. "Page at the National Assembly of Niger website" (in Faransanci). Archived from the original on February 13, 2005. Retrieved 2013-10-02.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link).
  3. "GOUVERNEMENTS DU PRESIDENT MAHAMANE OUSMANE" Archived 2007-10-21 at the Wayback Machine, official web site of the Nigerien presidency (in French).
  4. "List of deputies elected in the 1999 parliamentary election by constituency". Archived from the original on July 18, 2004. Retrieved 2004-07-18.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link), National Assembly website (2004 archive) (in French).
  5. ""LISTE DES Députés PAR GROUPE PARLEMENTAIRE"". Archived from the original|archive-url= requires |url= (help) on July 18, 2004. Missing or empty |url= (help); |access-date= requires |url= (help), National Assembly website (2004 archive page) (in French).
  6. "List of commissions in the National Assembly". Archived from the original on July 18, 2004. Retrieved 2015-11-02.CS1 maint: BOT: original-url status unknown (link), National Assembly web site (2004 archive page) (in French).