Omotayo Aramide Oduntan (haihuwar 5 ga watanYuni, 1957), ƴar siyasan Nijeriya ne da ke wakiltar Mazaɓar Alimosho II a Majalisar Dokokin Jihar Legas a ƙarƙashin inuwar jam’iyyar All Progressives Congress.[1]

Omotayo Oduntan
Rayuwa
Haihuwa jahar Legas, 5 ga Yuni, 1957 (67 shekaru)
ƙasa Najeriya
Karatu
Matakin karatu diploma (en) Fassara
Harsuna Turanci
Pidgin na Najeriya
Sana'a
Sana'a ɗan siyasa
Imani
Jam'iyar siyasa All Progressives Congress

Rayuwa da aiki

gyara sashe

An haife ta ne a jihar Legas, kudu maso yammacin Najeriya, inda ta kammala karatun ta na firamare da sakandare. Tana da takaddar difloma da difloma kan Tsabtace Abinci da Kula da Abinci (Food Hygiene and Food Handling) daga makarantar Royal Institute of Public Health. Ta taba zama babbar Mataimakiya ta Musamman ga Gwamnan Jihar Legas a kan Matsalolin asali a yayin da take aiki a matsayin ‘yar Majalisar Dokokin Jihar Legas daga 1999 zuwa 2003 sannan kuma daga 2011 zuwa 2015.[2] A yanzu haka tana matsayin Chief Whip na majalisa ta 8 a majalisar dokoki na jihar Legas.[3]

  1. Joshual, Prince (May 5, 2016). "Lagos lawmaker supports Senate on capital punishment for kidnappers". Champion Newspaper. Archived from the original on April 4, 2017. Retrieved April 4, 2017.
  2. "Lagos Assembly probes monarch – The Nation Nigeria". The Nation. February 12, 2014. Retrieved April 4, 2017.
  3. "Woman of the Sun: politics taught me patience, perseverance –Oduntan, Lagos deputy chief whip – The Sun News". The Sun. Retrieved April 4, 2017.

Hanyoyin haɗin waje

gyara sashe