Olena Apanovych
Rayuwa
Haihuwa Dimitrovgrad (en) Fassara, 9 Nuwamba, 1919
ƙasa Kungiyar Sobiyet
Ukraniya
Mutuwa Kiev, 21 ga Faburairu, 2000
Makwanci Baikove Cemetery (en) Fassara
Karatu
Makaranta H.S. Skovoroda Kharkiv National Pedagogical University (en) Fassara
Matakin karatu Candidate of Historical Sciences (en) Fassara
Harsuna Harshan Ukraniya
Sana'a
Sana'a Masanin tarihi da Ma'adani
Wurin aiki Kharkiv, Ufa (en) Fassara, Kiev da Southern Kazakhstan (en) Fassara
Employers Central State Historical Archives of Ukraine in Kyiv (en) Fassara  (1944 -  1950)
Institute of the History of Ukraine (en) Fassara  (1950 -  1972)
Kyaututtuka
Mamba National Academy of Sciences of Ukraine (en) Fassara
National Writers' Union of Ukraine (en) Fassara

Olena Apanovych ( 'yar kasar Ukraine) (9 Nuwamba 1919 - 21 Fabrairu 2000) masaniyar tarihice 'yar Yukren, mai bincike na Zaporozhian Cossackdom. Ta karɓi kyautar Antonovych.

Tarihin Rayuwa

gyara sashe

An haifi Olena Apanovych a Melekes na gundumar Simbirsk (yanzu Dimitrovgrad na Ulyanovsk Oblast ), Rasha, a cikin dangin magatakarda na tasar jirgin kasa. Ta hanyar tunawa da danginta, mahaifiyarta ta haifi Olena a cikin motar jirgin kasa. Mahaifinta ya kasance manoma daga kasar Bularus (saboda haka sunan karshe na mutanen Belarus Apanovich) mahaifiyarta kuma ta kasance daga dangi masu ƙaramin marta daga kasar Poland. Ta kwashe duk yarintarta a Manchuria (arewa maso gabashin China) inda mahaifinta ya yi aiki. Jafan sun koro danginta daga China. Sun zauna a Kharkiv a shekarar 1933, inda Olena ta gama sakandare. Mahaifiyar Olena ta mutu ba da daɗewa ba kuma an kama mahaifinta a 1939 dangane da zargi na ƙarya.

A shekarar 1937, ta shiga cikin "All-Union Institute of Journalism" a Moscow, amma makarantar da aka rufe nan da nan kuma Apanovych komo Kharkiv inda ta sauke karatunta a Pedagogical Institute (Sashen Harsuna Rasha harshe da wallafe-wallafe) ba da dadewa ba kafin fara yakin duniya na biyu. Bayan fara mamayewar Jamus an mayar da ita zuwa Kazakhstan da Bashkiria. Daga watan Mayun, 1944, Olena ta yi aiki a Central State Archive na Ukraine da ke a Kiev a matsayin mai bincike da kuma ta shiga shirye-shiryen da yawa na tattara tarihi don wallafa su.

A cikin shekara ta 1950, Apanovich ta kare karatun ta na digiri na Kandidat of Science (kimanin Ph.D. daidai) akan shigar Zaporozhian Cossacks yakin Russo-Turkish na 1768-1774 kuma ya shiga Cibiyar Tarihin Cibiyar Kimiyya ta Ukraine a matsayin bincike na musamman a kan Cossackdom. A tsakanin shekarun 1950-72, ta kafa bulaguro na tsoffin kayan tarihi na kasa zuwa wuraren da ke da alaka da tarihin Zaporozhian Cossackdom, ta buga ayyuka da dama na kimiyya, kuma sanya cikakken rajista na wuraren tunawa da Zaporozhian Cossacks.

Daga 1972, bayan an kore saboda dalilai na siyasa daga Cibiyar Tarihi, Apanovych ta yi aiki a Cibiyar Kimiyya ta Tsakiya ta Cibiyar Kimiyya ta Ukraine, ta ba da gudummawa na mahimman a cikin binciken rubutun hannu. A farkon shekaru tamanin, ana yawan gayyatarta a matsayin masaniyar tarihi a don ba da shawara ga fina-finai na gaskiya da almara akan Cossackdom na Ukrainian.

Kyaututtuka da karramawa

gyara sashe
  • 1991, Apanovich ta zamo memba na Kungiyan Marubutan Kasar Yukren
  • 1994, an bada lambar yabo na sunan T.Shevchenko
  • 1995, Lamban yabo na Antonovych a USA

Manazarta

gyara sashe
  • Tarihin rayuwar Apanovych akan gidan kayan gargajiya na rukunin motsi, (in Ukrainian)
  • Lyudmyla Tarnashynska, "shekaru 55" karkashin alamar Clio." , Dzerkalo Tyzhnia, (The Weekly Mirror), Satumba 4-10, 2004.